Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800
Published: 7th, November 2025 GMT
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki.
Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa.
Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage adadin zuwa 800 bayan jerin tattaunawa masu zafi da Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa da Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki da Ƙungiyoyin Kwadago.
Wata majiya daga cikin ma’aikatan AEDC ta ce shugabannin kamfanin sun fara da shirin korar 1,800, amma sun rage zuwa 800 bayan matsin lamba daga ƙungiyoyin, waɗanda a farko suka dage cewa ba a kamata a kori kowa ba.
“Shugabanni sun so su kori 1,800, amma bayan matsin lamba, sun rage zuwa 800. Tun da farko kungiyoyin sun nemi kada a kori kowa,” in ji ma’aikacin da ya nemi a boye sunansa don kauce wa hukunta shi.
“Ƙungiyoyin sun fara da cewa kada a kori kowa, amma daga baya an ce sun amince da 800. Ma’aikatan da abin ya shafa sun kamata su fara karɓar takardunsu daga ranar Litinin, amma an jinkirta, sai jiya aka fara ba su takarda,” wata majiya ta bayyana.
Wata takardar sallama mai taken “Sanarwar Sallama Daga Aiki”, da aka rubuta a ranar 5 ga Nuwamba, 2025, kuma Adeniyi Adejola, Babban Jami’in Kula da Ma’aikata na kamfanin, ya sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa aikin na daga cikin “shirin daidaita ma’aikata da ake ci gaba da aiwatarwa.”
Takardar ta kuma bayyana cewa duk ma’aikatan da abin ya shafa za su karɓi haƙƙinsu bayan kammala tsarin sallamar su.
Wani ɓangare na takardar ya ce: “Muna bakin cikin sanar da kai cewa ba za a sake buƙatar ayyukanka a kamfanin nan ba daga ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025. Wannan shawara ta biyo bayan sakamakon aikin daidaita ma’aikata da kamfanin ke aiwatarwa. Ka tabbata cewa an yanke wannan shawara bayan dogon nazari da kuma bisa ka’idojin kamfanin.”
“Ana buƙatar ka kammala tsarin sallama a wurin aikinka, ka kuma dawo da duk wani kayan kamfani da ke hannunka kafin ka mika kanka ga wakilin kula da ma’aikata. Kammala waɗannan matakai ne zai ba da damar sarrafa kuɗin sallamarka,” in ji takardar sallamar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rage ma aikata
এছাড়াও পড়ুন:
Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan TinubuA cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu.
Duk da ƙoƙarin jama’a na ceto yarinyar kafin isowar jami’an hukumar kashe gobara ya ci tura, saboda zurfin rijiyar da kuma yawan ruwan da ke cikinta.
Sai dai daga bisani an tsamo gawarta, sannan aka miƙa ta ga dagacin yankin, Abdullahi Garba.
Sai kuma a Larabar ce makamancin wannan lamari ya auku, inda wani yaro mai shekara shida, Ahmad Abdurashid, ya faɗa rijiya a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck da ke a ƙaramar hukumar Dala.
An dai samu nasarar ceto yaron a raye amma daga bisani ya ce ga garinku nan.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya bayyana baƙin ciki kan faruwar irin waɗannan lamurra, yana mai roƙon jama’a da su riƙa rufe rijiyoyi da kyau da kuma kula da yara ƙanana domin guje wa irin wannan mummunan sakamako.