Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa
Published: 7th, September 2025 GMT
Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar.
Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a — MURICOginni ya yi Allah wadai da korar ɗan majalisar, yana mai cewa babu wata hujja kuma ba su ba da izini ko wani iko na ɗaukar wannan hukunci ba.
Sunday ya ce tuni an sallami shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa tare da rukunin tsagin Kwankwasiyya daga jam’iyyarsu ta NNPP.
A bayan nan ne Hashim Dungurawa ya bayyana cewa sun kori ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji saboda dalilai na cin amana da kuma tallan wani ɗan takara.
“Mun same shi da cin amanar jam’iyya a matakai daban-daban,” in ji Dungurawa.
“Na farko, mun same shi da tallata ɗantakarar shugaban ƙasa na wata jam’iya da ba namu ba.
“Na biyu, ya ce zai iya fita daga jam’iyyar. Wannan ba ƙaramin cin amana ba ne. Na uku, ba ya biyan kuɗin haraji na jam’iyya, duk da cewa akwai doka cewa duk wata akwai abin da zai bayar domin ci gaban jam’iyyar.
“Na huɗu, ba ya zuwa mazaɓarsa. ‘Yan mazaɓarsa kan yi kusan wata biyar ba su ji ɗuriyarsa ba.”
Na amince da hukuncin —KofaA martanin da mayar, Abdulmumi Jibrin Kofa ya sanar da ya amincewa da matakin korarsa da jam’iyyar ta yi.
Sai dai ya bayyana mamakin wannan hukuncin da jamiyyar ta yanke. “Ina da maganganun da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba, amma duk da haka ina nan a kan batuna, babu abin da na janye” in shi.
Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, “ko a gidan soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kare kansa.
“Game da batun rashin biyan kuɗina, ina roƙon jam’iyya ta turo min da lissafin kuɗin nan, zan biya nan take. Babu buƙatar hayaniya ko cin mutunci.”
Ya ce ya so a ce ya ci gaba da zama a jam’iyyar, “amma tun da jam’iyyar ta kore ni, dole in amince da matakin da ta ɗauka.”
Dan majalisar ya ce nan gaba kaɗan zai sanar da matakin da zai ɗauka a game da makomarsa a siyasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya.
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wutaA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja, wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, da kuma jaddada muhimmancin Ibadan a siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.
“Na kai ziyara don girmama sabon Olubadan, Rashidi Ladoja, wanda ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma attajiri za ta taimaka wajen ɗaga martabar Ibadan,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa tattaunawarsa da Obasanjo da Ladoja na da nasaba da ci gaban Najeriya da kuma shugabanci da ke da burin sauya al’umma ta fuskar gaskiya da adalci.
Ziyarar Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ake hasashen zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.