Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-05@11:05:13 GMT

Matan 500 Za Su Amfana da Gwajin Cutuka Kyauta a Jihar Gombe

Published: 5th, November 2025 GMT

Matan 500 Za Su Amfana da Gwajin Cutuka Kyauta a Jihar Gombe

Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku.

Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara.

Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata.

Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da wuri shi ne hanya mafi tasiri wajen rage mace-macen da ke da alaka da cutar sankara, tana jan hankalin mata da su daina jira sai alamun cuta sun bayyana kafin su nemi likita.

A nasa bangaren, Dr. Bawa Gift, Babban Likita (Senior Registrar) a Sashen Tiyata na Asibitin FTH Gombe, ya bayyana sankarar nono a matsayin cutar sankara da ta fi yawaita a tsakanin mata a duniya, tare da gargadi cewa karuwar yawan masu kamuwa da ita na kara zama babbar barazana ga lafiyar al’umma.

Ya ce wani binciken shekara ta 2022 ya tabbatar da cewa gano cutar da wuri da kuma kula da ita cikin lokaci na iya kara tsawon rayuwar marar lafiya, ko da ba a iya warkarwa gaba daya ba.

Dangane da sankarar mahaifa, Dr. Halima Faruk, Farfesa Mai Dangi (Associate Professor) a fannin Gynaecologic Oncology na FTH Gombe, ta bayyana cutar a matsayin “daga cikin cututtukan sankara mafi yawan yiwuwa a kare su amma mafi nauyi ga mata” a duniya.

Ta bayyana cewa kimanin sabbin mutane dubu 500 ke kamuwa da cutar sankarar mahaifa a duk shekara a fadin duniya, fiye da rabinsu na rasa rayuwa, musamman a kasashe masu karamin karfi irin su Najeriya.

Hudu Shehu Ibrahim/Gombe

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: cutar sankara

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ta kara da cewa, matakin gaggawa da ya dace Sin da Amurka su runguma, shi ne aiwatar da muhimmiyar matsaya da aka cimma, yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a Busan na kasar Koriya ta Kudu, da ingiza karin daidaito cikin harkokin raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayyar Sin da Amurka, da ma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka November 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
  • Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Waɗanda Rikici Ya Shafa A Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa
  • Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa