Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher

Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan.

A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen.

Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in jin kai da ba a taba ganin irinsa ba. UNICEF ta bayyana cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan da aka yi bincike a kansu, a yayin da fada ke kara kamari da kuma kwararar ‘yan gudun hijira a Darfur.

A cikin rahotonta, UNICEF ta kara da cewa ta gudanar da bincike a wurare 88 tsakanin watan Janairu da Yuli na wannan shekarar, inda ta bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na Darfur, musamman a arewacin yankin, sun sami karuwar rashin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa na kashi 15 cikin 100.

Rahoton ya tabbatar da cewa adadin yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki ya karu zuwa sama da 315,000 a rabin farko na shekarar, karuwar kusan kashi 48 cikin 100 idan aka kwatanta da wannan lokacin a bara. Yayin da matsalar abinci ke ƙara ta’azzara, haka nan wahalar waɗanda suka ƙaura daga El Fasher zuwa Tawila a Arewacin Darfur ke ƙaruwa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon   November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan

Ana ci gaba da tattara gawarwakin mutane da mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai DaukinGaggawa suka kashe a jihar Arewacin Kordofan na kasar Sudan.

Kungiyar Likitoci na Kasar Sudan ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da tattara gawawwakin mutane a Arewacin Kordofan, bayan da mayakan Rappid Support Forces suka farma yankunan a kokarin da suke yi na kwace iko da jihar baki daya.

Kungiyar Likitoci ta Sudan ta bayyana cewa, tana bin diddigin manyan laifukan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces suke aikatawa kan fararen hula marasa makamai a birnin Bara da ke jihar Arewacin Kordofan.

Kungiyar ta tabbatar da cewa: Gawawwaki da dama sun taru a cikin gidaje a cikin birnin, kuma mayakan Rapid Support Forces  suna hana iyalan waɗanda abin ya shafa kusantar ‘yan uwansu da suka mutu.

Adadin mutanen da suka ɓace kuma yana ƙaruwa kowace rana, tare da rufe kafafen sadarwa gaba ɗaya kuma babu ingantaccen wurin kiwon lafiya ko jin kai a cikin birnin.

Kungiyar Likitoci ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, ƙungiyoyin agaji, da al’ummar duniya da su ɗauki matakin gaggawa don dakatar da waɗannan take hakki, a buɗe hanyoyin masu tsaro ga fararen hula don samun tserewa zuwa wuraren masu aminci, da kuma ba iyalai damar binne gawawwakinsu cikin mutunci.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka    November 4, 2025 Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu November 4, 2025 Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci November 4, 2025 Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda  Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Matsalar Jin Kai A Falasdinu, Inda Falasdinawa Miliyan 1.5 Suke Cikin Halin Musiba Da Bala’i
  • Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar
  • Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani
  • Najeriya: Ta Sake Jaddada Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar
  • Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba
  • Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar HDL  Da Taimakon Rundunar RSF
  • Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka
  • China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump
  • Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan