Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
Published: 6th, November 2025 GMT
A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar gina ingantaccen yankin ciniki cikin ’yanci na tashar ruwa ta Hainan ko FTP a takaice. Shugaba Xi ya bayyana bukatar ne yayin dake sauraron rahoton aiki game gina yankin na FTP a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
A cewarsa, gina yankin FTP na Hainan muhimmiyar manufa ce ta kwamitin kolin JKS, wadda aka tsara domin zurfafa cikakkun sauye-sauye, da bude kofa ga waje a sabon zamani.
Shugaban na Sin ya kara jaddada bukatar kyautata nazari, da aiwatar da ka’idojin aiki na cikakken zama karo na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, tare da kokarin cimma burikan da aka sanya gaba, dangane da bunkasa yankin FTP na Hainan a dukkanin fannoni, ta hanyar lura da tsare-tsare, da aiki tukuru da wanzar da kwazon aiki.
A ranar 18 ga watan Disamban bana ne yankin FTP na Hainan, zai kaddamar da ayyukan kwastam na musamman na daukacin tsibirin, matakin da shugaba Xi ya ce zai kasance jigon matakai da kasar Sin za ta aiwatar, don fadada bude kofa mai inganci, da ingiza gina budadden tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, sarkin Spaniya Felipe VI, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, daga ranar 10 zuwa 13 ga watan nan na Nuwamba. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA