Kungiyar Kwallon Kafa Ta Matan Najeriya Ta Samu Nasara Akan Takwararta Ta Moroko Da Kwallaye 3-2
Published: 27th, July 2025 GMT
Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata.
A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda su ka ci kwallaye 2-0, sai dai bayan komawa hutu, ‘yan wasan na Najeriya sun farke kwallon da aka zura musu, sannan kuma su ka kara da daya akai.
Sai dai duk da cewa an sami galaba akan kungiyar kwallon kafar ta Moroko, magoya bayanta da suke bakin ciki, sun jinjinawa kungiyar tasu.
Wasu sun bayyana cewa ba su tsammaci za a sami galaba akansu ba,, domin sun yi wasa da kyau,to amma da alama sun zakalkale wajen jin cewa za su nasara, kamar yadda wata ta fadawa kafar watsa labaru ta ‘Africa News”.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.