Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Published: 8th, November 2025 GMT
Kasashen Mexico da Iran sun yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Ofishin jakadancin Iran da ke Mexico ya yi watsi da “iƙirarin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi game da wargaza wani makircin da Iran ta shirya na kashe jakadan Isra’ila a Mexico.”
A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Iran ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙirƙirar kafofin watsa labarai da kuma ƙarya bayyananna da nufin lalata dangantakar abokantaka da tarihi tsakanin ƙasashen biyu (Mexico da Iran),” yana mai jaddada kin amincewa da ikirarin tare da bayyana shi a matsayin makircin makiya a fili.
A nata ɓangaren, hukumomin Mexico sun fitar da wata sanarwa suna cewa: “Ba su da wani rahoto game da wani yunƙuri da ake zargin an yi wa jakadan Isra’ila a Mexico na neman kashe shi.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran.
A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da bukatu da Iran ba za ta taba amincewa da su ba.
Iran ta yi maraba da tattaunawa amma Pezeshkian ya sake nanata cewa, a yanzu ba Iran ce za ta tabbatar da gaskyarta ba, domin ta riga ta yi haka, ya rage kan kasashen turai ne su tabbatar wa duniya cewa da gaske suke yi a cikin abin da suke furtawa.
Duk da haka, ya ce, Iran na ci gaba da fuskantar zarge-zarge marasa tushe da kuma ƙarin takunkumi a ƙarƙashin hujjar cewa tana hankoron kera mkaman nukiliya.
Pezeshkian ya jaddada cewa za a iya magance matsaloli ne kawai ta hanyar tattaunawa da mutunta juna, ba ta hanyar tilastawa ko barazana ba.
“Inda za a iya magance rashin fahimta ta hanyar yin amfani da hankali, me ya kawo maganar yin amfani a karfi da kashe-kashe da rusa gine-gine da ababen mor rayuwa na al’ummar kasa.
A nasa bangaren, Macron ya gode wa Pezeshkian saboda matakan da aka dauka don aiwatar da yarjejeniyoyin da suka gabata kuma ya bayyana niyyarsa ta yin aiki don samar da sabon tsari na tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Yammacin duniya.
Ya ce ci gaba da tattaunawa yana da mahimmanci don gina gaskiya da aminci, da dage takunkumi, da kuma inganta dangantakar kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci