Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
Published: 7th, November 2025 GMT
Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna tsoron wanda zai yi tunani a gaba, saboda duk wanda ya kawo wani ilimi sai ka ji an ce Zindiki ne, sai a so a halaka shi ma idan ba a yi wasa ba.
To da aka soma rubutun, China kamar su suka soma, to da buga littafi ilimi ya soma ya]uwa zuwa ga jama’a, ilimi ya fito daga dakin bauta, ya fito daga masarautar sarakuna ya shiga gidan kowa, a da kuwa yana gidan sarakuna ne kawai, ilimi ya soma yaduwa har Allah ya kawo Rediy,o tana daga cikin abin da ya yada ilimi, ta yi hobbasa wajen wayar da kan komai, dan haka a kula da rediyo yana da matukar kyau saboda galibin mutane rediyon nan ita ce hanyar daukar maganarsu, Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass (RA) da alkhairi, ya sha wahala wajen sa karatun Kurani a ciki, har Allah ya kawo talabijin, har “cable” din nan ta zo, yanzu fa za ka iya ganin duniya a cikin abu, karshen wayewa, karshen ci gaba a yanzu kuma wayar salula, wadannan wayoyi da suke hannunmu sun sa a yanzu babu jahili sai dai dakiki wanda ya ki sani da gangan, amma wayar nan babbar farfesa ce ta kowane karni, idan fannin jinya ne za ta fada ma har abin da hankalinka ba zai taba kawowa ba, haka a fannin alheri, idan fannin tarihi ne za ta kai ka har inda kudinka ba zai iya kai ka ba. Alhamdu Lillah, mun gode Allah.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: sai wanda ya
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA