Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gina Gadar Sama Da Ta Kasa A Mararraba
Published: 5th, November 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta samu amincewar gwamnatin tarayya domin gina sabbin gada biyu na sama da kuma ta karkashin kasa (under-pass) a yankin Mararaba da ke Karamar Hukumar Karu.
Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mr. Peter Ahemba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
A cewar Ahemba, gwamnati za ta fara aikin kafin gwamnatin yanzu ta kai ga karewar wa’adinta a shekara ta 2027. Ya ce tun da dadewa Gwamna Abdullahi Sule ya ware kudaden aikin, kafin ma a kammala tsarinsa.
Ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2019, gwamnatin jihar ta kan ** tabbatar da ajiyar kuɗi kafin fara kowanne babban aiki**, saboda dorewa da tabbatar da kammalawa akan lokaci.
Ahemba ya ce gina wadannan flyovers da under-pass ya zama dole sakamakon cunkoson ababen hawa da ke addabar yankin Karu–Mararaba, musamman ga mazauna da direbobi da matafiya.
“Wannan aiki zai magance matsalar cunkoso, ya inganta tafiyar ababen hawa, tare da ƙara ingancin hanyoyi,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamna ya bai wa Hukumar Nasarawa State Urban Development Agency (NUDA) umarnin gudanar da bincike da tantance wuraren da suka fi dacewa domin gina wadannan ayyukan.
Mr. Ahemba ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar fara aikin, ta kuma kammala shi kafin karewar wa’adinta a 2027.
Aliyu Muraki, Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba
A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA