Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
Published: 6th, November 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ce ƙofofinta buɗe suke ta sayar da dukkan matatun manta na Warri, Fatakwal da Kaduna ga ’yan kasuwa domin ƙarfafa gasa a fannin tace mai a Najeriya.
Mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wata hira da Bloomberg TV a gefen taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, ranar Talata.
Verheijen ta ce wannan mataki na daga cikin shawarwarin da ake dubawa don inganta harkar man fetur a Najeriya.
“Daya daga cikin matakan da za a iya la’akari da su kenan, musamman idan aka samu wanda yaje da kwarewa da kuma jarin da zai iya sayen su,” in ji ta.
Ta ce matatun man da a baya suka dade suna aiki a ƙarƙashin tallafin gwamnati, yanzu sun sami kishiyoyi bayan cire tallafin man fetur.
“Yanzu da muka cire tallafin, mun kawar da duk wani tarnaki da ke cikin wannan kasuwar ta man fetur,” kamar yadda ta fada.
A watan Oktoba, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) Limited ya sanar da fara cikakken bincike na fasaha da kasuwanci kan matatun mai guda hudu da gwamnati ke da su.
Tun a watan Yuli, Shugaban kamfanin Group, Bayo Ojulari, ya ce aikin gyaran matatun ya ɗan samu tsaiko, yana mai cewa kamfanin na fatan kammala sake duba su kafin ƙarshen shekara.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.
A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta.
Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta.
NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar MakamaiShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan