Sojin Amurka sun gabatar da shirin ƙaddamar da hari a Najeriya
Published: 6th, November 2025 GMT
Dakarun Sojin Amurka sun kammala shirye-shiryen kai hare-hare a Najeriya bayan umarnin da Shugaba Donald Trump, ya bai wa Ma’aikatar Tsaron ƙasar kan ɗaukar mataki game da zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Afirka (AFRICOM), ta gabatar da yadda hare-haren za su kasance.
Daga cikin shirin akwai kai wa ’yan ta’adda hare-hare da jiragen yaƙi da amfani da jirage marasa matuƙa.
Sannan kuma akwai tsarin haɗin gwiwa da sojojin Najeriya ta hanyar musayar bayanan leƙen asiri da tallafin kayan aiki.
Sai dai jami’an Ma’aikatar Tsaron Amurka sun yi gargaɗin cewa irin waɗannan hare-haren ba lallai su magance matsalolin tsaro a Najeriya ba.
Sun ce dole sai an gudanar da yaƙi mai faɗi kamar yadda aka yi a Iraƙi ko Afghanistan, sai dai sun ce hakan zai sa Amurka ta kashe maƙudan kuɗaɗe.
Trump, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da tin sakaci wajen “kisan Kiristoci,” kuma ya bayar da umarnin dakatar da sayar wa Najeriya makamai.
Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zargin, inda ta danganta matsalar tsaro da wasu abubuwa kuma tana shafar kowane ɓangare na addini.
Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Najeriya ba ta buƙatar sojojin Amurka su shiga ƙasarta, sai dai taimako a fannin leƙen asiri da kayan aiki, tare da buƙatar Amurka ta mutunta Najeriya.
Ƙasar China ta goyi bayan Najeriya, tare da gargaɗin Trump kan tsoma baki cikin harkokin da suka shafi ƙasa mai ’yanci.
Masana da tsofaffin Hafsoshin sojin Amurka sun yi gargaɗin cewa irin wannan farmaki zai iya ƙara ta’azzara matsalar tsaro.
Sun kuma bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ta samo asali ne daga ’yan fashi, rikicin filaye, da ta’addanci da ke shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dakarun Soji hare hare Najeriya yaƙi zargi
এছাড়াও পড়ুন:
China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump
China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci.
A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama.
Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido.
Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a game da gaskiyar lamarin kasar.
Da take mayar da martani ga tashin hankalin, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Mao Ning ta ce Beijing zata tsaya tsayin daka tare da Abuja.
Ta kara da cewa “China tana adawa da duk wata kasa da ke amfani da addini ko hakkin dan adam a matsayin hujja don tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe ko kuma yi musu barazana da takunkumi ko karfi,” in ji Mao.
Ta kara da cewa China tana goyon bayan gwamnatin Najeriya gaba daya wajen samar da ci gaba”.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci