HausaTv:
2025-11-08@12:20:52 GMT

 Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar

Published: 8th, November 2025 GMT

A yau Asabar ne jirgin  kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha.

 Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40.

 Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita  900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran.

Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da zai ratsa ta cikinsu, da hukumominsu na tashoshin jiragen kasa, jami’an shiga da fitar kaya, da kuma cibiyoyin kasuwanci.

Zuwan jirigin kasan na Rasha zuwa Iran, yana a matsayin bude sabon shafi a harkokin kasuwanci a tsakanin  kasashen biyu da kuma tsakanin Iran da kasashen Asiya ta tsakiya.

A baya a cikin watan Aprilu na wannan shekarar wani jirgin dakon kayar daga kasar China ya iso Iran,wanda shi ma yake a matsayin yunkurin bunkasa kasuwanci.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail November 8, 2025 Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin November 8, 2025 Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta November 8, 2025 Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025  Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi

Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba.

Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12.  

Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni.

A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu.

A yau, Iran tana cikin matsayi mafi kyau fiye da yadda take a ranar 13 ga Yuni.

Araghchi ya yi cikakken bayani game da kuskuren lissafin na abokan gaba, yana mai nuna hasashensu cewa Iran za ta yi sauri ta mika wuya a karƙashin matsin lamba na hare-hare ba zato ba tsammani.   

Hakika abokan gaba ba su cimma burinsu ba a lokacin wannan yakin na kwanaki 12 ba,inji shi..

“Manufarsu ta kaddamar da yakin ita ce su ba wa Iran mamaki da hare-haren ba zato ba tsammani, kuma sun yi tunanin Iran za ta mika wuya cikin kwana biyu ko uku,” in ji shi.

“Amma hakan bai faru ba saboda lura da Jagoran Juyin Juya Halin  Musulunci na Iran (Ayatollah Seyyed Ali Khamenei), wanda ya maye gurbin kwamandojin soji cikin sauri, da kuma jajircewar gwamnati na shawo kan rikicin da kuma kare muradun kasar.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Kwamitin Gwamnonin IAEA November 6, 2025 Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho November 6, 2025 Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar  Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE  Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya
  • Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin
  • Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza
  • Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
  • Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu
  • Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi
  • Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Kwamitin Gwamnonin IAEA
  • Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya