Leadership News Hausa:
2025-11-05@18:58:01 GMT

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Published: 5th, November 2025 GMT

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

 

Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.

(Tasallah Yuan)

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025 Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika November 4, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki.

A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana za ta kaddamar da matakan soji a Najeriyar.

To sai dai kuma a nata martani, ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar da wata sanarwa, wadda ke musanta zargin na Amurka, tare da jaddada cewa Najeriya na ci gaba da yaki da ayyukan masu tsattsauran ra’ayi, da kare rayukan ’yan kasar, da martaba rayukan mabiya mabambantan addinai da akidu, kana tana biyayya ga dokoki daidai da odar kasa da kasa.

Cikin amsar da ta bayar dangane da tambayar wani dan jarida, Mao Ning ta ce kasar Sin na adawa da wata kasa ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe na daban, ta hanyar fakewa da batun kare hakkokin addini ko na bil’adama. Kazalika, tana adawa da yawaitar barazanar kakaba takunkumai da amfani da karfin tuwo. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya November 4, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha November 4, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi
  • Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
  • Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
  • Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
  • An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
  • Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
  • Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
  • Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
  • Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar