Leadership News Hausa:
2025-11-07@11:46:53 GMT

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Published: 7th, November 2025 GMT

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru.

Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci.

A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci gaban dangantakar Sin da Kamaru, kuma yana fatan hadin gwiwa da shugaba Paul Biya, don aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing a bara, ta yadda za a inganta cikakkiyar alaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare masu zurfi, da kyautata rayuwar al’ummomin kasashen biyu. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano

Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu

A cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu.

Duk da ƙoƙarin jama’a na ceto yarinyar kafin isowar jami’an hukumar kashe gobara ya ci tura, saboda zurfin rijiyar da kuma yawan ruwan da ke cikinta.

Sai dai daga bisani an tsamo gawarta, sannan aka miƙa ta ga dagacin yankin, Abdullahi Garba.

Sai kuma a Larabar ce makamancin wannan lamari ya auku, inda wani yaro mai shekara shida, Ahmad Abdurashid, ya faɗa rijiya a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck da ke a ƙaramar hukumar Dala.

An dai samu nasarar ceto yaron a raye amma daga bisani ya ce ga garinku nan.

Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya bayyana baƙin ciki kan faruwar irin waɗannan lamurra, yana mai roƙon jama’a da su riƙa rufe rijiyoyi da kyau da kuma kula da yara ƙanana domin guje wa irin wannan mummunan sakamako.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas
  • Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
  • Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
  • Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha