Da marecen jiya Asabar ne dai sojojin HKI su ka kutsa cikin jirgin ruwan da yake dauke da masu fafutuka da su ka fito daga kasashe mabanbanta, wadanda suke son zuwa bagar ruwan Gaza domin kawo karshen killace yanki da aka yi tun 2006 da kuma kisan kiyashin da HKI take yi musu.

Kananan jiragen ruwa na sojojin HKI ne su ka nufi jirgin ruwan mai suna; “Hanzalah” sannan su ka kutsa cikinsa.

Bayan shigar sojojin cikin jirgin ruwan sun hau cikinsa sannan su ka fara  dukan mutanen da suke cikinsa.

 MAsu kula da jirgin na Hanzalah sun bayyana cewa; Sojojin HKI sun kame mutanen da suke cikin jirgi tare da yin awon gaba da su, zuwa wani wuri.

Dama tun da fari masu kula jirgin sun sanar da cewa, HKI ta yi musu barazanar kutsawa cikinsa.

Barazar sojojin yahudawan ta kunshi yin kira ga matukin jirgin da ya koma inda ya fito ko kuma a kutsa cikinsa da karfi.

Gabanin yankewar hanyoyin sadarwa da jirgin ruwan na “Hanzalah” an ji yadda yake yin kira na neman taimako.

Da akwai masu fafutuka 21 daga kasashe mabanbanta a cikin jirgin ruwan na “Hanzalah” da suke son kawo karshen killace Gaza da aka yi tun tsawon shekaru 17 da su ka gabata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: cikin jirgin ruwan

এছাড়াও পড়ুন:

 An Jikkata  Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota

Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam.

Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba.

Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne.

Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba.

Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake.

Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin, tare da yin kira a ci gaba da gudanar da irinsa da yawa.

Kungiyar Hamas ta ce, dole a tsammaci wannan irin harin, bisa la’akari da laifukan da HKI take tafkawa a Gaza da yammacin kogin Jordan.

Kungiyar Jihadul-Islami kuwa cewa ta yi, hari irin wannan yana kara tabbatar da yadda al’ummar Falasdinu ta sha alwashin ci gaba da riko da kasarta da kuma kalubalantar ‘yan mamaya da dukkanin abinda su ka mallaka.

Shi kuwa kwamitin gwagwarmaya na Falasdinu ta yi kira ne ga dukkanin  Falasdinawa da su yunkura domin fada da sojojin sahayoniya.

Ita kuwa kungiyar “Mujahidun-al-Falasdiniyya ta sa wa harin albarka tare da bayyana shi a matsayin babban sako ga ‘yan mamaya dake cewa martani akan kisan gillar da suke yi zai fadada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  An Kashe Sojojin HKI 3 A Yankin Khan-Yunus Na Gaza
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Furuci Da Halakar Sojan Guda Da Ya Jikkata A Zirin Gaza
  • Hanyoyin Gyaran Gashi
  • Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar
  • Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da “Kauracewar” Amurka
  • Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
  • Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
  •  An Jikkata  Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza