ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mutum 2 kan sukar shugaban karamar hukuma a Kano

An kama mutum biyu ’yan jam’iyyar NNPP a Karamar Hukumar Tofa da ke Jihar Kano, kan sukar Shugaban Karamar Hukumar, Ibrahim Yakubu Addis, a Facebook.

Wadanda da aka kama sun hada da Murtala Garba Doka da Shamsu Safiyanu Lambu wanda aka fi sani da Shamzeet Lambu.

Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa

Rahotanni sun bayyana cewar shugaban karamar hukumar ne ya bayar da umarnin kama su ne a ranar Litinin.

Shamzeet Lambu ya wallafa a Facebook, inda ya zargi shugaban karamar hukumar da kin kammala aikin titin Lambu zuwa Banki zuwa Yarimawa da Jakata, wanda gwamnatin jiha ta amince da shi kan kudi kimanin naira miliyan 240.

A rubutun da ya wallafa cikin harshen Hausa, Lambu ya ce: “Naira miliyan 240 kudinmu a Burji, Allah Ya saka mana.”

Rahotanni sun nuna cewa an fara tsare mutanen biyu a ofishin ’yan sanda na Tofa, kafin daga bisani aka mayar da su hedikwatar rundunar da ke kwaryar birnin Kano a Bompai domin ci gaba da bincike.

Shugaban matasa na yankin, Kwamared Nazifi Ado Lambu, ya tabbatar da kamen, inda ya ce hakan ya tayar da hankalin jama’a a yankin.

“E, an kama su saboda rubutun da suka yi a Facebook game da aikin titi. An tsare su a Tofa kafin daga bisani aka kai su Bompai,” in ji shi.

Wani mazaunin Lambu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce al’ummar yankin sun dade suna rokon shugaban karamar hukumar kan gyara titin.

“Ya taba yin alkawarin zai gina titin da bututun ruwa da kwalta, amma bayan gwamnatin jiha ta amince da aikin, sai aka tsaya a iya share titi da zuba yashi, sai kuma aka bar aikin,” in ji mazaunin.

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar, Ibrahim Yakubu Addis, ya ce shi ne ya kai kara ofishin binciken laifuka (CID) domin a tabbatar da gaskiyar zargin da ake yi masa.

“Ba mu yi musu komai ba illa tambayarsu su kawo hujjar zargin da suka yi. Mutane da yawa suna ganin abin da ake wallafawa a intanet, kuma ba wannan ne karo na farko da suke irin wannan ba,” in ji shi.

Ya kuma ce adadin kudin aikin da suke zargi ba gaskiya ba ne.

“Gwamna ya amince da aikin da kudi kasa da Naira miliyan 100, ba miliyan 240 ba.

“Mun dai ce su kawo hujja kawai,” in ji shugaban.

Kamen mutanen biyu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Karamar Hukumar Tofa, inda jama’a ke kira da a warware lamarin cikin lumana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
  • Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
  • Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta
  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
  • Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya
  • Kwamitin Tsaron Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza
  • An kama mutum 2 kan sukar shugaban karamar hukuma a Kano
  • Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro