CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Published: 7th, November 2025 GMT
Kafar yada labarai ta CGTN da ke karkashin babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta kaddamar da wasu tashoshi uku a dandalin FAST yau Alhamis 6 ga watan Nuwamba, da ke kunshe da tashar CGTN Global Biz, da ta China Travel, da ta Discovering China. Wadannan tashoshin za su gabatar da shirye-shiryen talabijin zuwa ga masu kallo kusan miliyan 200 a duk fadin duniya, bisa wasu manyan dandalolin FAST guda 15, alamarin da ya shaida babban ci gaban da CMG ya samu a bangaren gabatar da shirye-shirye zuwa sassan kasa da kasa.
Shirin talabijin bisa dandalin FAST, sabon salo ne wanda ya bulla cikin sauri a ’yan shekarun nan a kasuwar shirye-shiryen bidiyo ta duniya, shirin da ya kunshi nau’o’in abubuwa daban-daban bisa goyon-bayan tallace-tallace, kana, babu bukatar masu kallo su biya. (Murtala Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE November 5, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025
Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025