Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A FCT
Published: 6th, November 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya November 6, 2025
Labarai Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu November 6, 2025
Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari November 6, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Waɗanda Rikici Ya Shafa A Jihar
Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar UINL Da FHFL Sun Gina Gidaje 100 Ga Mutanen Da Rikici Ya Raba Da Muhallans
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da Family Homes Funds Ltd (FHFL), bisa tallafin Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Tarayyar Najeriya, sun kammala ginin gidaje 100 domin mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma marasa galihu a cikin jihar.
Wannan aiki ya gudana ne a yankin Rigachikun, inda kamfanin Ummi International Nigeria Ltd ya bayar da fili, yayin da Gwamnatin Kaduna, Family Homes Funds, da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare suka ɗauki nauyin ginin gidajen gaba ɗaya.
A yayin ƙaddamar da ginin da kuma miƙa ma waɗanda za su zauna, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa aikin ya samo asali ne daga kudirin gwamnatinsa na taimaka wa waɗanda suka rasa matsuguninsu sakamakon rikice-rikice, tare da dawo musu da martabar rayuwa.
Gwamna Uba Sani ya ce wannan aiki yana cikin shirin gwamnatin jihar na inganta walwalar marasa galihu da tabbatar da ci gaban da ya shafi kowa a fadin jihar.
A nasa jawabin, Ministan Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, ya yabawa wannan haɗin gwiwa tare da tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da yin aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin agaji domin cimma burin ci gaba mai ɗorewa.
Ita kuma tsohuwar Ministar Mata ta Tarayyar Najeriya, Dame Pauline Tallen, ta bayyana ginin a matsayin wani muhimmin aiki na alheri wanda zai taimaka wajen farfaɗo da rayuwar zawarawa, marayu da sauran masu buƙata a cikin al’umma.
A nata bangaren, Dr. Umma Sani (Zinariyar Gabasawar Zazzau), shugabar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd, ta bayyana cewa gidauniyarta ta dade tana gudanar da irin wannan aiki na samar da matsuguni ga zawarawa da marayu domin inganta rayuwar su kamar sauran jama’a.
Ta kuma gode wa Gwamna Uba Sani bisa cikakkiyar gudunmawar da ya bayar wajen ganin an samu wannan nasara, tare da bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin al’umma da tausayi.
Haka kuma Ambasada Dr. Fatima Mohammed Goni, shugabar Global Business Network Initiative (GBNI), ta bayyana Dr. Umma Sani a matsayin abin koyi ga mata a Najeriya, la’akari da yadda ta ke aiwatar da ayyukan jin kai don tallafa wa mabukata.
Ta kuma yi kira ga wadanda suka amfana da gidajen da su kula da su da kyau, domin tabbatar da dorewar manufar da aka samar da su saboda ta alheri ce ta gaskiya.
Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a yau Litinin, inda ya sami halartar manyan baki, jami’an gwamnati, da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu daga sassa daban-daban na Jihar Kaduna.