HausaTv:
2025-11-07@08:20:04 GMT

An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas

Published: 7th, November 2025 GMT

An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé.

Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai.

Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa.

Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi.

Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon   November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar HDL  Da Taimakon Rundunar RSF

Jakadan Saudan a MDD Hassan Hamid ya bayyana cewa; KAsarta tana yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kara matsin lamba akan HDL wacce take bai wa rundunar RSF makamai da sauran kayan soja.

Hamid wanda ya gabatar da taron manema labaru ya ce: ” Afili yake cewa daga ina ne rundunar RSF take samun makamai,abin takaici kuwa ba daga ko’ina ba ne sai HDL.

Jakadan na kasar Sudan  a MDD ya yi kira da dakatar da bai wa wannan kungiyar ta ‘yan ta’adda makamai, ba tare da bata lokaci ba.

A can kasar Sudan ana ci gaba da fadace-fadace musamman a yankin Darfur.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta MDD ta fitar da bayanin dake cewa; ta sami rahotanni masu tayar da hankali, da su ka hada da yi wa mutane kisan gilla.

A baya sojojin kasar Sudan sun zargi rundunar kai daukin gaggawa ta RSF tana samun taimako daga HDL da makamai da kuma ‘yan ina da yaki daga kasashen Chadi, Libya, Kenya da Somaliya.

Daga cikin laifukan da ake zargin rundunar ta “Kai Daukin Gaggawa” da aikatawa da akwai cin zarfin mata da yi wa fararen hula kisan kiyashi sannan da wawason dukiyar mutane.

A ranar 26 ga watan Oktoba ne dai mayakan rundunar kai daukin gaggawar su ka kutsa cikin birnin Al-fasha, Babbar cibiyar yankin Darfur.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa November 5, 2025 Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi  November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar HDL  Da Taimakon Rundunar RSF
  • DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa
  • An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla
  • Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU
  • Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba
  • Mataimakin Tsohon Shugaban Kasar Amurka Dick Cheney Ya Mutu A Yau Talata
  • Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci