Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai
Published: 6th, September 2025 GMT
Iyayen ɗalibai a sassan arewacin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ta ƙara kuɗin makaranta da kuma tsadar littattafai a kowace shekara, da sauran hanyoyin da suka ce makarantu ke tatsar kuɗi a hannunsu.
Wasu makarantu masu zaman kansu kan tilasta wa iyaye sayen littattafai daga wurinsu kawai, alhali a kasuwa ana samun su a farashi mafi sauƙi.
Malama Halima Mu’azu, mazauniyar Hayin Malam Bello a Kaduna, wadda ke da yara a makarantar kuɗi, ta ce: “A wannan zangon makarantar ’ya’yana sun ƙara kuɗi sosai. Babbar ’yata da ke aji ɗaya na sakandare yanzu za ta shiga aji biyu, amma sun ƙara kuɗin daga N27,000 zuwa kusan N32,000. Wannan ƙari ya zo ne a daidai lokacin da rayuwa ta yi tsada sosai.”
Ta ƙara da cewa, makarantar firamare ma ta ƙara kuɗi sosai. “A baya, daga aji ɗaya zuwa uku ana karɓar kusan N30,000. Amma yanzu sai ka tanadi sama da N200,000 a zangon farko idan aka haɗa da kuɗin PTA, fom, takardu da sauran kayan makaranta. Wannan babban matsin lamba ne a kanmu iyaye.”
An haramta wa makarantu tilasta wa iyaye sayen sabbin litattafai duk shekara a Filato ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsayeA cewarta, hakan yakan jefa iyaye cikin damuwa saboda duk bayan wata uku sai su biya kuɗin da ya kai kusan N100,000.
“Ka ga wannan yana nufin iyaye marasa ƙarfin aljihu cinbashi ko kuma su ja baya wajen biyan wasu buƙatun gida.”
Tsawwala kuɗi barkataiShugaban Ƙungiyar Iyaye da Malamai ta Ƙasa (PTA), Danjuma Muhammad, ya ce: “Makarantu masu zaman kansu sun ɗauki kansu tamkar ’yan kasuwa. Akwai makarantun kuɗi da ba su cancanci a kira su makarantu ba, saboda ba su da rajista. Amma duk da haka suna karɓar kuɗaɗen da suka fi na makarantu masu inganci.
“Wasu makarantu ma ba su da lasisi, amma suna karɓar kuɗaɗen da suka wuce hankali. Idan gwamnati ta rage musu haraji, to za mu ga sauƙi.”
Amfani da littafi sau ɗayaWani magidanci daga Hayin Ɗanmani, Badamasi Isah, ya bayyana cewa tsarin littattafan da ake amfani da su yanzu wata hanya ce ta cin kuɗi.
“A zamaninmu idan ɗan uwa ya gama amfani da littafi sai ya bar wa ƙaninsa. Amma yanzu an tilasta cewa sai ɗalibai su yi rubutu kai tsaye a cikin littafin, wanda hakan ke hana a sake amfani da shi.
“Misali, littafin Lissafi ko Turanci ya kamata a yi amfani da shi na tsawon shekaru, amma yanzu idan aka yi rubutu a ciki, sai an sayi sabo. Wannan rashin adalci ne ga iyaye.”
Tsadar littafi a makarantuYa ƙara da cewa, makarantu sukan tsawwala farashin littattafai sama da na kasuwa.
“Littafin da a kasuwa yake N10,000, a makaranta za ka saya da N16,000. Sannan suna tilasta sai a wurinsu za a saya. Wannan mataki yana ƙara damuwar iyaye ne kawai.”
Sauya bangon littafiAbdulganiyu Abdurrahman Giwa, mamallakin makarantar Igra Model Standard a Sabon Gari, ya shaida cewa: “Wasu makarantu suna canza bangon littafin duk zangon karatu don hana amfani da tsohon littafi. Wannan gaskiya yana jefa iyaye cikin wahala saboda yawanci ba su da ƙarfin biya.”
Sai dai a cewarsa, ba laifin masu makarantu kaɗai ba ne, domin gwamnati ma tana da rawar takawa.
“Gwamnati na ƙara haraji, mu kuma dole mu ɗora wa iyaye. Haka kuma wasu masu buga littattafai suna kawo irin da ba su daidaita da na kasuwa, shi ya sa muke tilasta wa iyaye su saya daga makaranta.”
A hana sayen sababbin littattafai duk shekaraWani ɗan Najeriya, Mustapha Bulama, ya yi kira ga gwamnatin Kaduna da majalisar dokoki da su hana makarantu tilasta sayen sababbin littattafai duk shekara.
Ya ce babban dalili shi ne yadda ake sa yara su yi rubutu kai tsaye a littafin karatu maimakon amfani da ‘workbook’.
Ya lissafa matsalolin da hakan ke jawowa:
– Nauyin kuɗi ga iyaye da ke da yara da dama.
– Yara suna koyan sakaci da littattafai.
– Rashin adalci tsakanin iyalai masu ƙarfin kuɗi da marasa shi.
– Rushe manufar ilimi mai araha da daidaito.
Tsadar bukukuwan yaye daliɗaiAminiya ta ruwaito cewa iyaye suna yawan kokawa bisa yadda makarantu musamman na kuɗi suke tsadar kuɗaɗe a hannunsu da sunanan bukukuwan yaye ɗalibai ciki har da masu kammala ajin raino zuwa firamare da kuma masu kammalawa ƙaramar sakandare zuwa babbar sakandare.
Daga cikin abin da ke musu tuwo ƙwarya shi ne tsadar ƙudin bukukuwan da kuma tsirfar da makarantun ke ɓullo da shi na tufafi masu tsada da ɗaliban ke sanyawa da kuma cewa dole sai a makarantun za a yi.
Rawar ƙungiyar PTAShugaban PTA na ƙasa, Danjuma Muhammad, ya ce iyaye suna da ƙarfi idan suka tashi tsaye, “Makarantu suna da ikon ƙara kuɗi, amma idan PTA ta nuna rashin amincewa, gwamnati dole ta shigo ta duba lamarin. Wannan shi ne mafita.”
Koken iyaye mataHajiya Halima Abdullahi Sani daga Malali Gabas ta ce:
“Yarinya ta fara makaranta shekaru biyu da suka wuce muna biyan N60,000. Yanzu muna biyan N190,000 da littattafai da sauran kuɗaɗe. Wannan ya ninka fiye da sau uku cikin ƙanƙanin lokaci. Idan aka ƙara da kuɗin mota, sai ya zama nauyi mai tsanani.”
Game da littattafai, ta ce: “Zai fi kyau a maimaita su saboda yawanci ba su cika amfani da su ba. Don haka matakin wasu gwamnoni na hana tilasta sabbin littattafai duk shekara abin a yaba ne.”
Sabbin matakan gwamnatiBayan irin waɗannan koke-koke daga iyaye da ƙungiyoyi, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ɗauki sabon mataki.
A ranar 2 ga Satumba, 2025, Hukumar Kula da Ingancin Makarantu ta jihar (KSSQAA) ta fitar da sanarwa inda ta haramta wasu al’adu da ta ce suna ƙara wa iyaye nauyin kuɗi ba tare da dalili ba.
Gyara kan littattafai masu rubutuDaga ranar 1 ga Satumba, 2026, hukumar ta ce masu wallafa littattafai za su daina buga littattafan da ake rubuta a ciki.
Darakta Janar na hukumar, Farfesa Usman Abubakar Zaria, ya ce, “Wannan dabi’a na jefa iyaye cikin ƙarin kashe kuɗi ba dole ba, kuma tana haifar da asara. An umurci masu wallafa littattafai da su samar da workbooks dabam don rubuce-rubuce, yayin da littafin asali ya ci gaba da kasancewa abin da ake iya sake amfani da shi,” in ji hukumar.
Ƙarin kuɗi ba bisa ƙa’ida baKSSQAA ta kuma gargaɗi masu makarantu da su guji ƙarin kuɗi ba tare da izini ba.
“Duk wani ƙarin kuɗi dole ya samu amincewar PTA tare da cikakken quorum da bayanan ɗalibai. Duk wanda ya karya wannan ka’ida zai fuskanci hukunci mai tsauri,” in ji Farfesa Zaria.
Takƙaita bikin yaye ɗalibaiYa kuma ya bayyana cewa daga yanzu, ɗaliban JSS 3 (Basic 9) da SS 3 (Senior Secondary) kawai za su yi bukukuwan kammala karatu.
“An lura cewa wasu makarantu suna shirya bukukuwan kammala karatu ga kowace aji, kuma suna tilasta wa iyaye biyan kuɗi. Wannan dabi’a tana hana gwamnati cimma manufarta ta rage tsadar ilimi da inganta samun damar karatu ga kowane yaro,” in ji sanarwar.
Hukumar ta kuma hana al’adar “sign-out” inda ɗalibai ke yin hargitsi da rashin ladabi bayan jarabawar ƙarshe.
“Yawaitar wannan dabi’ar ta rashin ladabi, hargitsi, da rashin tsaro daga dalibai yayin bikin ya zama abin damuwa,” in ji Farfesa Zaria.
An shawarci makarantu da su samar da madadin bikin, kamar taron ban kwana, nune-nunen basira, ko miƙa tutar jagoranci, waɗanda za su bai wa ɗalibai damar murna cikin tsari da mutunci.
Sabbin matakan gwamnati sun fito ne a daidai lokacin da iyaye ke ƙara korafi kan tsadar ilimi da hanyoyin tatsar kuɗi a makarantu.
Yanzu ana sa ran ƙa’idojin za su rage wa iyaye radadin kashe kuɗaɗe barkatai, tare da tabbatar da ingantaccen tsarin karatu a Kaduna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Kuɗaɗe makarantu tilasta wa iyaye wasu makarantu su makarantu duk shekara a makarantu a makaranta ƙara kuɗi
এছাড়াও পড়ুন:
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya nemi sabbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance duk wata barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu da ma wadda ka iya kunnowa nan gaba.
Shugaban ya gargadi sabbin hafsoshin tsaron cewa ’yan Nijeriya sakamako kawai suke buƙata, ba uzuri ba, saboda haka dole ne su cika aikin da aka ɗora musu.
Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026 Ƙwallo ta kashe ɗan wasan CricketTinubu ya bayyana hakan ne bayan bikin ƙara wa sabbin hafsoshin tsaron da shugabannin rundunonin soji girma da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis a Abuja.
A cewarsa, “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma, da wasu sassa a Kudanci.”
A ranar Laraba ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro; Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa; Rear Admiral Idi Abbas Hafsan Sojan Ruwa; Air Marshall Kennedy Aneke Hafsan Sojan Sama; da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye a matsayin Shugaban Tattara Bayanai na Soja.
“Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin.
“’Yan Najeriya suna sa rana ganin sakamako, saboda haka babu wani uzuri da za su karɓa. Ina kuma kira da ku kasance masu dabaru da hangen nesa da kuma jarumta.
“Mu kasance mun tari hanzarin duk waɗanda ke neman tayar da zaune tsaye a ƙasarmu,” in ji Tinubu.
Yayin bikin, an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa Janar, Waidi Shaibu zuwa Laftanar Janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa Air Vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa Laftanar Janar.