Bakaken Fatar Amruka Da Suke Yin Hijira Zuwa Afirka Suna Karuwa
Published: 27th, July 2025 GMT
Ana samun Karin bakaken fatar Amurka da suke baro kasar suna dawo wa nahiyar Afirka domin samun kyakkyawar rayuwa a cikinta.
Mafi yawancin bakaken fatar suna nuna rashin gamsuwarsu da yanayin tattalin arziki da kuma siyasa na Amukra da su ka taka rawa wajen sa su, daukar matakin komawa Afirka da can ne asalin kakanninsu.
Wani dan kasar Amurka da ya rika yawo a tsakanin kasashe mabanbanta na Afirka a karshe ya tare a kasar Kenya, ya bayyana yadda yake jin ya saje a cikin nahiyar Afirka fiye da a can Amurka.
Auston Holleman wanda ya shahara da wallafa sakwanni a You Tube ya kara da cewa; Dukkanin mutane a Afirka sun yi kama da juna, ba kamar acikin turai, ko yankin Latin ba. “
Holleman ya kuma bayyana cewa yanayin siyasar Amruka a halin yanzu ya sa kasar tana fada da duk duniya baki daya.
Tun a 2019 ne dai kasar Ghana ta kaddamar da wani shiri na jawo hankalin bakaken fata a ko’ina suke a duniya domin samun wurin zama a cikinta.
A shekarar 2024 Ghana din ta ba da izinin zaman ‘yan kasa ga bakaken fata 524,mafi yawancinsu daga kasar Amurka.
Tun bayan da kamfanonin bakaken fata na Amurka irin su Adilah su ka koma Ghana, an sami karuwar bakaken fatar da suke komawa can.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Kutsa cikin Jirgin Ruwan “Hanzala” Dake Son Karya Killace Yankin Gaza
Da marecen jiya Asabar ne dai sojojin HKI su ka kutsa cikin jirgin ruwan da yake dauke da masu fafutuka da su ka fito daga kasashe mabanbanta, wadanda suke son zuwa bagar ruwan Gaza domin kawo karshen killace yanki da aka yi tun 2006 da kuma kisan kiyashin da HKI take yi musu.
Kananan jiragen ruwa na sojojin HKI ne su ka nufi jirgin ruwan mai suna; “Hanzalah” sannan su ka kutsa cikinsa. Bayan shigar sojojin cikin jirgin ruwan sun hau cikinsa sannan su ka fara dukan mutanen da suke cikinsa.
MAsu kula da jirgin na Hanzalah sun bayyana cewa; Sojojin HKI sun kame mutanen da suke cikin jirgi tare da yin awon gaba da su, zuwa wani wuri.
Dama tun da fari masu kula jirgin sun sanar da cewa, HKI ta yi musu barazanar kutsawa cikinsa.
Barazar sojojin yahudawan ta kunshi yin kira ga matukin jirgin da ya koma inda ya fito ko kuma a kutsa cikinsa da karfi.
Gabanin yankewar hanyoyin sadarwa da jirgin ruwan na “Hanzalah” an ji yadda yake yin kira na neman taimako.
Da akwai masu fafutuka 21 daga kasashe mabanbanta a cikin jirgin ruwan na “Hanzalah” da suke son kawo karshen killace Gaza da aka yi tun tsawon shekaru 17 da su ka gabata.