Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo
Published: 27th, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.
Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.
Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi UsmanA taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna.
Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda.
Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Taron ya samu halartar wakilan makiyaya da na manoma, ‘yan majalisa, shugabannin ƙananan hukumomi da na al’umma, ciki har da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Darazo da Ganjuwa.
A yayin taron, Gwamna Bala, ya sanar da kafa kwamitin bincike don gano dalilan rashin jituwa a tsakanin makiyaya da manoma.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ware hekta 2,500 na daji a domin ayyukan noma.
Ya nuna damuwarsa cewa wasu jami’ai da sarakunan gargajiya na raba filaye ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnan, ya gargaɗi manoma da ke karɓar filaye daga gwamnati amma suna bayar da su haya.
Ya ce: “Idan ba za ku yi noma da gonakin da aka ba ku ba, gwamnati za ta karɓe su ta bai wa waɗanda za su yi amfani da su.”
Ya ce gwamnati ba za ta amince da tashin hankali ba, kuma za ta ƙara ƙarfafa sasanci da tsaro domin samar da zaman lafiya.
Shugabannin Fulani, Malam Bala da Ahmadu Laddo, sun koka cewa manoma suna ƙoƙarin ƙwace filayen kiwo, kuma a wasu lokuta ana kai wa matansu hari.
Sun ce sun kai ƙara wajen ‘yan sanda da sarakunan gargajiya, amma babu abin da ya sauya.
Wakilan manoma, Mallam Lawal Babayo da mai unguwa Nadada, sun zargi makiyaya da kai musu hari da hana su noma a gonakin da gwamnati ta ware musu.
Wasu sun ce sun karɓi gonaki haya don noma, amma yanzu sun kasa noma, kuma hakan zai hana su samun amfanin gona.
Sun ƙara da cewa shekarun baya sun samu girbi mai yawa a gonakin da ke Darazo da Sade, amma bana rikici ya hana hakan.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sani Omolori, ya ce an tura jami’ai don tabbatar da doka da oda a yankin.
Masu jawabai a wajen taron sun yaba da matakin gwamnan, sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen wanzar da zaman lafiya a Jihar Bauchi.
Sun roƙi a ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar sasancin.
Ga hotunan yadda taron ya gudana:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Darazo Gwamna Bala Makiyaya makiyaya da
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.
Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa.
“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya.
Ya ce: “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” in ji Kwankwaso.
Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.
Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke Arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a Kudancin ƙasar.
Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.
“Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba,” in ji shi.