Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu
Published: 5th, November 2025 GMT
Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.
A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa.
Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano
Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi.
An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba.
An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — TrumpShugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44.
Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da ke mayar da hankali kan harkar noma, kuma mun himmatu wajen inganta ci gaban yankunan karkara.
“Mun ƙaddamar da wannan shiri mai taken ‘Gangamin dawo da yara makaranta’ a matsayin wata hanya ta nuna cewa ilimi da noma su ne ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.”
Ya ƙara da cewa, “Mun zo da wannan tunani ne domin taimaka wa al’ummar da ke sauraron shirye-shiryenmu saboda Allah.
“A matsayina na shugaban kafar yaɗa labarai, mun ga cewa ba wai kawai mu riƙa fallasa matsalolin da ke cikin harkar ilimi ba ne, amma mu ma za mu iya taka rawa wajen kawo sauyi.”
Daga nan sai ya buƙaci sauran ƙungiyoyi da kamfanoni da su yi koyi da irin wannan aiki a matsayin gudummawarsu ga ci gaban ƙasa.
Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano, Musa Saleh Kwankwaso, ya gode wa gidan rediyon bisa wannan hoɓɓasan da ya yi, tare da roƙon sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da shi.
“Ilimi haƙƙin kowa ne, gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin komai ita kaɗai ba. Irin waɗannan ƙungiyoyi da mutane su ma su shigo su taimaka. Muna farin ciki da wannan mataki da Himma Radio ta ɗauka,” in ji Hakimin.
Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, wanda shi ma ya halarci bikin, ya ce Najeriya da ke da yawan jama’a sama da miliyan 200, waɗanda kuma fiye da rabinsu matasa ne, akwai buƙatar haɗa kai wajen tallafa wa fannin ilimi.
Ya kuma tabbatar da cewa ƙofar jami’arsa a buɗe take don haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki don ganin ta bunƙasa ilimi musamman a yankunan karkara.