Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu
Published: 6th, November 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan
Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa.
A cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillacin labaran Iran ‘IRNA’ bayan ya isa birnin Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, a safiyar Laraba, Qalibaf ya ce: “Iran da Pakistan, a matsayin kasashe makwabta, suna jin dadin hulda daban-daban a fannin tattalin arziki, siyasa, da kuma harkokin majalisa, musamman idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki a dangantakar kasashen biyu da kuma yanayin yankin.”
Ya kara da cewa: “Kasashen biyu suna mai da hankali kan hadin gwiwar kasuwanci, siyasa, da tsaro, tare da hadin gwiwa mai inganci tsakanin hukumomin gwamnati a Tehran da Islamabad.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Gwamnonin IAEA November 6, 2025 Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho November 6, 2025 Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran da Pakistan
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi
Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba.
Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12.
Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni.
A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu.
A yau, Iran tana cikin matsayi mafi kyau fiye da yadda take a ranar 13 ga Yuni.
Araghchi ya yi cikakken bayani game da kuskuren lissafin na abokan gaba, yana mai nuna hasashensu cewa Iran za ta yi sauri ta mika wuya a karƙashin matsin lamba na hare-hare ba zato ba tsammani.
Hakika abokan gaba ba su cimma burinsu ba a lokacin wannan yakin na kwanaki 12 ba,inji shi..
“Manufarsu ta kaddamar da yakin ita ce su ba wa Iran mamaki da hare-haren ba zato ba tsammani, kuma sun yi tunanin Iran za ta mika wuya cikin kwana biyu ko uku,” in ji shi.
“Amma hakan bai faru ba saboda lura da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (Ayatollah Seyyed Ali Khamenei), wanda ya maye gurbin kwamandojin soji cikin sauri, da kuma jajircewar gwamnati na shawo kan rikicin da kuma kare muradun kasar.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Kwamitin Gwamnonin IAEA November 6, 2025 Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho November 6, 2025 Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci