Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya
Published: 8th, November 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki.
Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa.
Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.”
Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da hatsari.
A gefe daya, kasar Afirka Ta Kudu ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike akan yadda aka yi ‘yan kasarta 17 su ka shiga yakin, bayan da su ka aike da sako suna neman a taimaka musu su koma gida.
Shugaban kasar ta Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, ‘yan kasar da su ka tafi yakin matasa ne da shekarunsu suke a tsakanin 20 zuwa 39,bayan da aka shafa musu zuma a baki na samun aiki mai tsoka.
A watan da ya gabata ma dai kasar Kenya ta sanar da cewa da akwai ‘yan kasashenta da ake tsare da su a cikin sansanonin sojan Rasha,bayan da su ka shiga cikin rikicin ba tare da saninsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar November 8, 2025 Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail November 8, 2025 Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin November 8, 2025 Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta November 8, 2025 Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru.
Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci.
A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci gaban dangantakar Sin da Kamaru, kuma yana fatan hadin gwiwa da shugaba Paul Biya, don aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing a bara, ta yadda za a inganta cikakkiyar alaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare masu zurfi, da kyautata rayuwar al’ummomin kasashen biyu. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA