Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai
Published: 6th, November 2025 GMT
Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama
A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.
Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.”
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji.
Ya ce, “Taron ya samar da dama don daidaita dabaru da tabbatar da cewa rundunar sojin sama tana ci gaba da zama ginshiƙi wajen tsaron ƙasa.”
Aneke, ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai a tsakanin sojin sama, sojin ƙasa, sojin ruwa da sauran hukumomin tsaro domin samun nasara tare.
Ya ce dole ne hare-haren su kasance bisa bayanan sirri da kuma tsari mai kyau don cimma sakamako mai ɗorewa.
Shugaban sojin sama ya tabbatar da cewa za su inganta walwalar jami’ai tare da ba su ƙarin horo da kayan aiki na zamani domin ƙara musu ƙwarewa a fagen fama.
Haka kuma ya yi alƙawarin bai wa ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha muhimmanci a cikin ayyukan rundunar.
Hakazalika, Aneke ya tabbatar da cewa rundunar sojin saman za ta ci gaba da mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki cikin ladabi, mutunci da ƙwarewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Dabarun Aiki Ruwan Bama bamai ruwan wuta taro Tsaro tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA