Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Published: 9th, November 2025 GMT
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka.
Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah
Wani sabon kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka ya nemi a hana ’yan kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore bizar shiga Amurka.
Kudurin, wanda dan majalisa Christopher Smith ya gabatar a ranar Talata, ya kuma bukaci kwace kadarorin mambobin kungiyar.
An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwaWannan na daga cikin matakan da gwamnatin Amurka ke ɗauka don dakile abin da ta kira take hakkin ’yancin addini ga Kiristocin Najeriya.
Kudirin dai na neman hukunta mutane da ƙungiyoyi da ke da hannu ko goyon baya wajen take hakkin ’yancin addini mai, a ƙarƙashin dokar kasa da kasa ta IRFA.
Christopher ya yaba wa Shugaba Trump bisa sake ayyana Najeriya a matsayin Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman, yana mai ambato rahotannin ci gaba da hare-hare kan al’ummomin Kirista a sassan ƙasar.
Kudirin ya kuma ambaci ’yan ta’adda Fulani da ke kai hare-hare a jihohin Binuwai da Filato a cikin kungiyoyin da ake sa’ido a kansu, wani matsayi da Amurka ke warewa ga ’yan ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da ake zargi da take hakkin addini.
Sauran irin wadannan kungiyoyin da aka ayyana a baya a ƙarƙashin dokar sun haɗa da Boko Haram, ISWAP, ISIS-Sahel, Taliban da kuma Houthi.
Idan aka amince da kudirin, zai bai wa hukumomin Amurka damar hana biza da kuma kulle kadarorin mutanen da ke da alaƙa da waɗannan ƙungiyoyi.
An gabatar da kudirin ne bayan watanni na kiraye-kirayen yin hakan daga ’yan majalisar dokokin Amurka da ƙungiyoyin Kiristoci masu tsattsauran ra’ayin.
Shugaban Amurka Donald Trump dai ya yi zargin ana yi wa Kiristoci a Najeriya kisan kiya, amma gwamnatin kasar ta yi fatali da zarge-zargen inda ta kira shi a matsayin na karya.