Leadership News Hausa:
2025-11-08@21:27:55 GMT

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Published: 8th, November 2025 GMT

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”.

 

Somalia (1992–1994)

Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s.

A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya.

Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida.

Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen sama a kan mayakan al-Shabab kuma ta hada kai da gwamnatin Somaliya domin dakile AlShabab.

A watan Janairu 2024 an bayar da rahoton cewa Amurka ta kashe ‘‘yan kungiyar AlShabab uku ba tare da yin wata gagarumar barna ba.

Bugu da kari, a watan Fabrairun 2025, Donald Trump ya ce ya umarci a kaddamar da hari ta sama kan wasu jagororin kungiyar IS da ke arewacin Somalia.

 

Laberiya (2014–2015)

A lokacin da cutar Ebola ta bulla a yammacin Afirka, Laberiya ta kasance cikin kasashen da cutar ta fi shafa. Amurka ta tura sojoji da kayan aiki domin taimakawa wajen dakile yaduwar cutar.

Wannan ya hada da gina cibiyoyin kula da marasa lafiya, jigilar kayan agaji, da horar da ma’aikatan lafiya.

Sai dai kuma a shekaru gabanin samun ‘yancin kai da bayan samun ‘yancin kai, Amurka ta tura dakaru zuwa kasar domin dakile yakin basasa da yan kasar suka kwashe shekaru suna fama da shi.

 

Senegal (2014–2015)

Senegal ta kasance cibiyar hadin gwiwa a lokacin barkewar cutar Ebola. Amurka ta tura sojojinta domin su bayar da tallafi na kayan aiki da kiwon lafiya don hada kai a matakan yanki.

Wannan ya taimaka wajen hana cutar ta mamaye bangaren kiwon lafiya da ya riga ya kasance da rauni a Senegal da kasashen makwabta.

 

Kenya (1998)

Bayan harin ta’addanci da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka a Nairobi, wanda ya hallaka mutane 224, ciki har da Amurkawa 12 da kuma jikkata fiye da mutum 1000, Amurka ta tura sojojinta don bayar da agajin gaggawa, kula da marasa lafiya, da tallafawa wajen ceto rayuka.

Aikin ya fi mayar da hankali kan jin-kai da bincike.

 

Tanzaniya (1998)

Harin ta’addanci da ya shafi Kenya ya kuma shafi Dar es Salaam a Tanzaniya, kamar yadda aka yi a Nairobi, sojojin Amurka sun shiga don kula da wadanda abin ya shafa, da tallafawa wajen kare yankin daga fadawa cikin rudani, da gudanar da binciken harin kamar yadda Amurkar ta yi ikirari.

 

Libya

Sojojin Amurka sun taba kasancewa cikin Libya ta hanyoyi daban-daban, suna shiga su taya yaki da kungiyoyi irin su ISIS tare da goyon bayan kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Haka kuma akwai lokutan da Amurka ta shiga kai tsaye: kamar harin soji da ta yi a shekarar 1986 da kuma fitowarta a cikin yakin 2011 da ya kawo karshen mulkin shugaban Muammar Ghaddafi.

Bugu da kari, tun daga watan Nuwamban 2015 har zuwa 2019, Amurka da kawayenta sun kaddamar da hare-hare ta sama da amfani da jirage marasa matuki a Libya lokacin yakin basasar da ya balle tun bayan faduwar gwamnati Muammar Ghaddafi a 2011.

 

Jamhuriyar Nijar

Kasancewar sojin Amurka a Jamhuriyar Nijar ya hada da tura dakaru na musamman da jiragen yaki marasa matuka don taimaka wa gwamnatin Nijar da Faransa wajen yaki da kungiyoyin ta’addanci a karkashin Operation Juniper Shield.

Ba a san girman adadin sojin Amurka a Nijar ba sosai har sai da aka yi harin Tongo a 2017, inda ‘yan kungiyar ISGS suka kashe sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu, lamarin da ya jawo tambayoyi da muhawara game da dalilin da ya sa Amurka ta ajiye sojoji sama da 800 a Nijar a wancan lokaci.

A 2024 ne hedikwatar tsaro ta Pentagon ta sanar da cewa za ta kammala kwashe dakarunta daga Jamhuriyar ta Nijar ya zuwa tsakiyar Satumban shekarar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Kuma a ranar 7 ga watan Yulin ne Amurkar ta kammala kwashe dukkannin sojojinta daga sansanin da ake kira da 101, inda kuma ragowar 500 da ke sansanin 201 suka fice daga kasar a ranar 5 ga watan Agustan 2024.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Labarai Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal November 8, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Amurka ta tura sojoji

এছাড়াও পড়ুন:

Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar.

An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa

“Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan ƙasa.

“Amma ba ma cikin yanayin firgici. Muna mayar da martani cikin natsuwa, hankali, da kuma la’akari da muradun ƙasarmu, tare da duba damuwar da ke cikin gida da waje dangane da halin da ake ciki. Amma zan sake jaddadawa, Najeriya ƙasa ce mai ba da ’yancin yin addinai,” in ji ministan.

Ya kuma ce gwamnati na mayar da martani kan waɗannan batutuwa ta hanyar kiyaye mutunci da darajar ƙasar, da kuma haɗin gwiwa da kowa, ciki har da ƙasashen duniya, don magance wannan matsala.

“Muna da iyakoki masu sauƙin shigowa, shi ya sa muke da fahimtar juna da makotanmu. Haka kuma muna da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kuma Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa. Mun fara magana da gwamnatin Amurka. Hanyoyin sadarwar mu a bude suke. Muna so a warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya.

“Baya ga siyasar lamarin, muna ɗaukar batun da muhimmanci. Amma ina so in ƙara jaddada cewa gwamnati, tun kafin abubuwan da suka faru a kwanakin baya, ta jajirce matuƙa wajen tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce amintacciya ga kowa.

“Shin akwai matsalolin tsaro a ƙasa? Eh, akwai. Shin ana kashe mutane a wasu sassan ƙasa? Eh. Amma shin gwamnati na yin wani abu don dakile hakan? Eh, tabbas akwai. Shin gwamnati na mayar da martani? Eh, tana yi. Amma ana yin hakan cikin cikakken hanyoyin da suka dace, tare da kiyaye daidaito da ake buƙata don fuskantar waɗannan matsaloli kai tsaye,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iraki Na Samu Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
  • An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa