Aminiya:
2025-11-18@11:02:29 GMT

HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja

Published: 2nd, October 2025 GMT

Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai.

A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27.

2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai

Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta.

Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja.

Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram Ɗalibai hare hare Kagara kwaleji Makaranta

এছাড়াও পড়ুন:

NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 

Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum.

Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu.

Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata.

Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin rayuwa. Jimillar kuɗin da aka fitar ya kai Naira biliyan 116.”

Sawyer ya ce har zuwa yanzu NELFUND biya dalibai 624,000 da suka riga suka fara karɓar kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.

Shugaban NELFUND ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen saka jari na zamantakewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.

Ya ce manufar shirin ita ce kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai ci gaba da karatu, tare da tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.

Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da gudanar da shirin cikin gaskiya da inganci, musamman ganin yadda yawan ɗaliban da ke amfana yake ƙaruwa a kullum.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
  • NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
  • Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba
  • Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
  • Sanusi ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
  • HOTUNA: Yadda Babban Taronjam’iyyar PDP ke gudana