Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita

Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita.

Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici.

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja

An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin.

A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban Limamin yana damunsa a mafarki.

An ce ya sha gaya wa abokai da danginsa cewa limamin ne ke haddasa tabarbarewar lafiyarsa ta hanyar sihiri.

“Yayin da lafiyarsa ke ƙara tabarbarewa, mutane suka fara yarda da zargin nasa. Da ya mutu, wasu matasa suka yanke shawarar cewa limamin ne ke da laifi,” in ji wata majiya daga yankin.

A ranar Laraba, rikici ya ƙara ƙamari yayin da ’yan uwan mamacin – Mohammed Shaba, Mamudu Gana, da Ndakpotun Issa, suka tara wasu matasa don tunkarar limamin.

Duk da ƙoƙarin wasu dattawa na kwantar da hankali, gungun matasan sun kai wa limamin hari, inda suka lakada masa duka har ya ce ga garinku nan.

“Sun afka wa limamin suna zarginsa da kashe Gana ta hanyar sihiri. Sun ƙi sauraron duk wanda ya yi ƙoƙarin dakatar da su,” in ji wata majiyar.

’Yan sanda daga ofishinsu na Tsaragi sun isa yankin bayan faruwar lamarin, inda suka kama wasu da ake zargi da jagorancin harin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, tana mai bayyana shi a matsayin “kisan gilla mai ban tsoro.”

Ta ce binciken farko ya nuna cewa bayan mutuwar Gana mai shekaru 25 a ranar 4 ga watan Nuwamba, ’yan uwansa Mohammed Shaba da Mahmud Gana sun zargi Babban Limamin da haddasa mutuwarsa, kuma suka tara wasu don kashe shi.

A cewarta, “An kama mutane huɗu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran da suka shiga lamarin.”

Ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya yi alla-wadai da lamarin, yana mai gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Tuni da aka yi jana’izar limamin bisa koyarwar addinin Musulunci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya
  • An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano
  • Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
  • Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 
  • Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
  • An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 
  • Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio
  • Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa