NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
Published: 15th, September 2025 GMT
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar.
A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a cikin shekarar nan, lamarin da ke nuna yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jami’anta sun kama mutanen ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, bayan sun samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano su.
NDLEA ta bayyana cewa ƙwayoyin Tramadol ɗin da aka gano an shigo da su ne cikin kwalaye a matsayin maganin multivitamins, yayin da ake ƙoƙarin fitar da su daga filin jirgin a wasu manyan motoci.
“Ƙwayoyin da aka kama ba su da wata alaƙa da amfani na lafiya, waɗanda aka shigo da su a ɓoye a matsayin maganin rage kasala da ƙara kuzari (multivitamins),” in ji sanarwar NDLEA.
Rahotanni sun nuna cewa a da likitoci na bayar da Tramadol ne don rage zafi da raɗaɗin ciwo, amma yanzu ta zamo annoba musamman a tsakanin matasa, wadda ke haddasa mummunan maye da illa ga lafiya.
Hukumar ta nuna damuwa game da yadda yawan masu amfani da Tramadol ke ƙaruwa ba wai a Najeriya kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashen Afirka, duk da illolin da ƙwayar ke haddasawa, kamar matsalolin taɓin hankali ko ma rasa rai gaba ɗaya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025
Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda October 30, 2025
Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025