Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar.
Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga
De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma.
Roma ce ƙungiyar da De Rossi ya kai zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar Europa League ta 2024, kafin a sallame shi bayan rashin nasara a wasanni hudu a jere a kakar da ta biyo baya.
A makon da ya gabata, Genoa ta kuma sallami daraktan wasanninta Marco Ottolini, inda ta maye gurbinsa da ɗan ƙasar Sifaniya, Diego Lopez.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Patrick Viera
এছাড়াও পড়ুন:
Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka
Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald
Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana kansa a
matsayin wanda ke gaba da Trump. Ya ce, “A wannan lokaci na duhun siyasa, New
York zai zama birni haske.” Ya ƙara da cewa, “Tare za mu kawo sauyi ga wannan zamani. Idan muka rungumi wannan sabuwar hanya ta jarumta maimakon mu gudu daga gare ta, za mu iya fuskantar mulkin masu kuɗi da na danniya da ƙarfin da suke tsoro, ba da sassaucin da suke nema ba.” Mamdani ya ci gaba da kalubalantar Trump kai tsaye: “Wannan ba kawai yadda za mu dakatar da Trump ba ne, har da wanda zai biyo bayansa. Don haka Donald Trump, tun da na san kana kallo, ina da kalmomi guda huɗu gare ka: Kara sauti.” Jawabinsa bai tsaya kan Trump kaɗai ba. Ya fara da ambaton Eugene Debs, wani ɗan gurguzu na ƙarni na 19 da 20, sannan ya yi alkawarin aiwatar da “tsarin da ya fi kowanne girma” don rage tsadar rayuwa a New York tun bayan zamanin Magajin Gari Fiorello LaGuardia kusan shekaru 100 da suka wuce. Mamdani ya doke Cuomo, wanda ya tsaya takara a matsayin ɗan mai zaman kansa bayan faduwa a zaɓen fidda gwani na Democrat a watan Yuni, da kusan maki 9. Dan takarar Republican Curtis Sliwa ya zo nesa da Mamdani. Magajin Gari Eric Adams, wanda ya tsaya takara a matsayin ɗan jam’iyya ta uku bayan nasararsa a 2021 a matsayin Democrat, ya janye a watan Satumba kuma ya goyi bayan Cuomo a watan da ya gabata. Wannan nasara ta Mamdani ta nuna yadda ya yi tasiri cikin siyasar New York cikin shekara guda, daga matsayin ɗan majalisar jiha da ba a san shi ba sosai, zuwa jagoran birni mafi girma a Amurka.