Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Published: 6th, November 2025 GMT
Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka.
Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda hakan ya karfafa daidaituwar alakar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka. Wannan ya tabbatar da cewa, Sin da Amurka suna da yakini a kan ci gaba da samun daidaito, girmamawa, da kuma cin gajiyar juna, kuma za su iya samun mafita a kan matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.
A nasu bangaren, membobin tawagar ta Amurka sun bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ta fitar da kayan noma na Amurka, kuma manoman Amurka suna girmama hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin, kana suna da niyyar hada hannu don fadada hadin gwiwa da kasar Sin. Sun kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa tsakanin kasar Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci ga cinikin kayan noma tsakanin kasashen biyu, kuma suna fatan ci gaba da samun kyakkyawan yanayin bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: tattalin arziki da cinikayya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro.
Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu.
Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan