Aminiya:
2025-11-02@06:20:15 GMT

’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista

Published: 12th, September 2025 GMT

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba.

Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN).

Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya

Adelabu, ya ce gwamnati ta samu nasarar samar da wutar lantarki da rarraba ta a matakin da ba a taɓa samu ba a tarihin ƙasar.

Ya bayyana cewa bunƙasa wutar lantarki shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin tana tallafa wa makarantu, asibitoci, masana’antu da kasuwanci.

Ya ƙara da cewa Najeriya na da ƙwarewa da ma’aikatan da za su iya ƙera mita, na’urar rarraba wuta da wayoyin lantarki a cikin gida domin dogaro da kai.

Sabbin gine-ginen da aka samar a NAPTIN za su taimaka wajen bai wa matasa damar samun ƙwarewa wajen inganta harkar wutar lantarki.

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da Gwamnatin Faransa ne suka tallafa da kuɗi da kuma shirye-shiryen horaswa.

EU, ta kuma bayar da tallafin Yuro miliyan 100 domin bunƙasa makamashi a Najeriya, wanda zai ƙara yawan megawat 400 nan da 2027, wanda zai amfanar da mutum sama da miliyan biyar.

Masana sun ce wannan zai ƙara samar da ayyukan yi tare da rage dogaro da man fetur.

Daraktan NAPTIN, Ahmed Nagode, ya ce wannan aiki wata sabuwar hanya ce ta samar da makoma mai kyau.

Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwa da ƙasashen waje zai bai wa matasan Najeriya damar koyon sabbin dabaru da shugabanci a fannin makamashi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya Wutar Lantarki wutar lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.

Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP

A lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.

Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.

A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.

Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .

Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.

Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.

Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.

Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.

Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.

Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.

Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar