Budurwa ta mutu a ɗakin saurayin da ke shirin auren ta a Abuja
Published: 11th, September 2025 GMT
Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata.
Majiyoyin ’yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar na fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta.
A cewar mjiyoyin, an samu takardar da ke dauke da rubutun magungunan da ake zaton na mai fama da cutar ne a dakin da lamarin ya faru.
Zagazola ya ce, “A ranar 9 ga watan Satumba, an samu rahoton wani lamari mai tayar da hankali na kisan kai a Gwagwalada, bayan wata mata mai shekaru 24 da aka gano sunanta Ebubechukwu Sunday Kelechi ta mutu ba zato ba tsammani a gidan saurayin da za ta aura.”
“Majiyoyi sun ce binciken farko na ’yan sanda ya nuna cewa tana fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta, kuma an samu magungunan cutar a wurin. Ba a ga wata alamar tashin hankali a jikinta ba.”
Makama ya kara da cewa an kama saurayin marigayiyar domin fadada bincike don gano ainihin musabbabin rasuwarta.
Lamarin Ebubechukwu dai ya kara yawan jerin matan da suka rasu a gidajen mazajensu ko samarinsu a cikin watannin baya-bayan nan a fadin Najeriya.
Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa yawancin irin wadannan abubuwan na faruwa ne yayin jima’i, yayin da wasu kuma ke da alaka da fada a tsakanin su ko kuma sanadiyyar tashin cututtukan da suke damun su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: budurwa Mutuwa Saurayi
এছাড়াও পড়ুন:
Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp