Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu
Published: 29th, September 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD.
A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba tare da kiyaye sharaɗin da NERD ta shar’anta ba.
A ƙarƙashin sabon tsarin wanda zai soma aiki daga 6 ga watan Oktoba, NERD ta wajabta cewa a yanzu rajistar ɓautar ƙasa tana ta’allaƙa ne da miƙa aikin binciken ɗalibai na kammala jami’a da sauran takardun bincike da ɗalibai suka saba gudanarwa a shekarar ƙarshe kafin kammala karatu.
Daga cikin abubuwan da ake buƙata daga ɗaliban Nijeriya a wannan sabon tsarin har da abubuwan da suka gudanar a makarantunsu, daga ciki har da kundin bincike na kammala karatu wato project.
Sakataren Gwamnati Tarayya, George Akume ne ya aika da wannan umarnin a cikin wata takarda ta musamman ga duka ma’aikatun gwamnatin ƙasar a ranar Lahadi a Abuja.
Sai dai wannan umarni ba zai shafi masu yi wa ƙasa hidima ba waɗanda suka fara hidimar ƙasar kafin a fitar da wannan sanarwar.
Akume ya bayyana cewa “na bayar da wannan umarnin domin kawo gyara tsarin yadda ake kiran ɗalibai aikin yi wa ƙasa hidima daidai da ƙa’idojin da ofishin shugaban ƙasa ya fitar na yin ɗa’a ga hukumar NERD.”
Kazalika, bayanai sun ce sabon tsarin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati wajen daƙile amfani da takardun bogi da kuma kare martabar ayyukan ’yan Najeriya.
Mai magana da yawun NERD, Haula Galadima, ta ce kowanne aiki zai ƙunshi cikakken sunan ɗalibi da na malamin da ya kula da aikin da shugaban sashen karatu da sunan makaranta.
Ta ce hakan zai ƙarfafa malamai su kula sosai da ɗalibai, domin sunayensu za su bayyana a wani dandalin dijital na duniya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP November 12, 2025
Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025
Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025