Aminiya:
2025-09-17@20:32:17 GMT

Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai

Published: 16th, September 2025 GMT

Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa.

Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce.

Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.

Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa.

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu An kama su kan satar zinarin Naira miliyan 110 a Kebbi

“Ba wai don su gudanar da jarrabawar aka kawo sojojin ba, sai don su kare ɗalibai da malamai daga duk wani cikas. Amma abin mamaki shi ne, me ya sa aka kawo sojoji maimakon ’yan sanda ko Sibil Difens?” in ji shi.

Shugaban ASUP na kwalejin, Kwamared Kolo Joshua, ya tabbatar da komawar su yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta yi biris da haƙƙoƙin malaman.

“Shekaru biyu ke nan muna jurewa, amma yau malaman suna bin bashin watanni 18 na kuɗin ƙarin aiki.

“Duk da tattaunawa da saƙonni da muka aika, ba a ɗauki mataki ba. Sai ma aka dakatar da ƙungiya sannan aka fara tsoratar da shugabanninmu da tambayoyi. Wannan ya jefa malaman cikin rashin kuɗi da raguwar ƙwarin guiwa,” in ji shi.

Ya ce sai dai idan gwamnati ta biya hakkokin malamai da kuma ta koma kan tattaunawa ta gaskiya ne za a samu zaman lafiya a makarantar.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Makarantar, Hussaini Mutammad Enagi, ya fitar, ta ce an dakatar da ayyukan ƙungiyar ne bisa dalilin “fargba da kuma rahoton tsaro mai tayar da hankali.”

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Malam Abubakar Dzukogi, ya musanta cewa sojoji aka kawo.

“Na zagaya duk cibiyoyin jarrabawa, ban ga sojoji ba. ASUP ne kawai suka shiga yajin aiki, sai makaranta ta ci gaba da gudanar da jarrabawar. Wannan lamari na farar hula ne, ba na soja ba,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jarrabawa Yajin aiki da jarrabawar kawo sojoji

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.

Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.

“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).

“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin