Aminiya:
2025-11-27@19:24:18 GMT

NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar bana

Published: 28th, September 2025 GMT

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci.

Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar

“Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar cewa ba Kano bace jiha mafi nasara, kamar yadda NECO ta bayyana a baya,” in ji rahoton.

Kazalika, binciken na Premium Times ya ƙara da cewa kwata-kwata Jihar Kano ma ba ta shiga cikin jihohi 10 da suka yi nasara ba, bal ma ta zo ne a matsayi na 29 daga cikin 37.

Sai dai NECO ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa alƙaluman da ta fitar sahihai ne, kuma an samo su ne bisa ingantaccen tsarin ƙididdiga da hukumar ke bi a duk shekara.

Ana iya tuna cewa, cikin sakamakon jarrabawar wannan shekara ta 2025 da Hukumar NECO ta fitar, ya nuna cewa kashi 60.26 cikin 100 ne suka samu kiredit biyar zuwa sama ciki har da darussan Lissafi da Turanci.

Shugaban hukumar Farfesa Ibrahim Wishishi ya shaida wa BBC cewa Jihar Kano ce kan gaba a yawan ɗaliban da suka samu nasara a jarrabawar a faɗin wuraren da hukumar ke shirya jarrabawar da suka haɗa da wasu ƙasashen Afirka.

Da take mayar da martani cikin wata sanarwa da gwamnatin Kanon ta fitar, ta ce wannan ne karon farko cikin shekara 25 da jihar ta samu wannan nasara.

Shugaban na NECO ya ce cikin ɗalibai 1,358,339 da suka rubuta jarrabawar, yayin da 818,492 ne suka samu kiredit a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jarrabawa Jihar Kano a jarrabawar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar.

A  jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024.

A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.

 

Ya jaddada cewa mutanen wadannan yankuna sun daɗe suna bukatar wannan aiki na hanyar.

Malam Umar Namadi ya ce titin zai ba su damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni mafi kusa cikin sauki.

Ya kuma ce yawancin wadannan hanyoyi sun kai matakin kammaluwa, kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da jerin bukukuwan kaddamar da su gaba daya.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a karkara domin saukaka samun hanyoyin shiga kasuwanni da birane.

Namadi ya bayyana cewa shirin tuntubar jama’a ya bai wa al’umma damar tattaunawa kai tsaye da gwamnati.

Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo Malam, ya ce titin na daga cikin hanyoyi 48 masu dauke da jimillar tsawon kilomita 977 da aka bayar a 2024 a kan kudi Naira biliyan 304.

Wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Abdullahi Musa da Malam Muhammad Gata, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan aiki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi