Aminiya:
2025-11-05@14:16:46 GMT

Ta yi garkuwa da kanta don karbar kuɗin fansa daga hannun mijinta

Published: 5th, November 2025 GMT

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗin fansa daga mijinta.

An kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin, wato Martins Chidozie mai shekaru 23 da Osita Godfrey mai shekaru 33.

Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150

Mataimakiyar Kakakin rundunar a jihar, ASP Eno Ikoedem, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan bincike kan wani rahoton garkuwa da aka kai wa ’yan sanda.

Ta ce a ranar 27 ga Oktoba, 2025, wani mutum mai suna Paul Adaniken ya kai rahoto a ofishin ’yan sanda na New Etete cewa ya bar matarsa, Chioma Success Ezebie, da ɗansu mai shekaru uku, Andrea Ojiezelabor, a gida kafin ya tafi shagonsa.

A cewarta, daga bisani an kira shi da wata lamba da bai sani ba, ana sanar da shi cewa an yi garkuwa da matarsa da ɗansa.

Mai magana da yawun rundunar ta ce masu garkuwa sun nemi a biya su kuɗin fansa naira miliyan 5 kafin su sako su.

Ta ce yayin bincike, an gano cewa ɗan uwanta, Osita Godfrey, wanda a baya ake zaton yana taimakawa da bayani, shi ma yana da hannu a cikin laifin, kuma an kama shi.

Ta ƙara da cewa bayanin da Godfrey ya bayar ya kai ga kama Chioma Success, wadda ta haɗa baki da abokan aikinta don ƙitsa garkuwa da kanta da nufin karɓar kuɗi daga mijinta.

Ta ce an kuma kama wani da ake zargi, Martins Chidozie, dangane da laifin.

ASP Eno Ikoedem ta tabbatar da cewa an kwato kuɗin fansar da aka biya na naira miliyan biyar, kuma yanzu haka an mika batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (SCID) domin ci gaba da bincike da gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garkuwa mai shekaru

এছাড়াও পড়ুন:

Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya

Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci.

Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota.

Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘YanSandan Jihar Kwara Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya
  • An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa
  • Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
  • Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha
  • Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza
  • Matar aure ta yanka wuyan mijinta, ta fasa masa ido da wuƙa a Neja
  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su