Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF
Published: 27th, July 2025 GMT
Wani rahoto daga ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa wato Medecins Sans Frontiere na nuni da cewa sama da yara 650 ne suka mutu bayan fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki a Jihar Katsina.
Medicins Sans Frontiere wadda ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki da aka isar da su zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da ƙungiyar ke da su a yankin.
A cewarta, a tsakanin Janairu da Yuni 2025 ta yi jinyar kusan yara 70,000 da ke fama da tamowa a Jihar Katsina, ciki har da kusan 10,000 da ke bukatar kulawa da ta dace daga likitoci .
“A wannan shekarar ta 2025 a cewar ƙungiyar, yara 652 suka mutu saboda rashin samun kulawa akan lokaci,” in ji Ahmed Aldikhari, mai magana da suna ƙungiyar ta MSF a Nijeriya, kamar yada sanarwa ta tabbatar a ranar Juma’a.
MSF ta ce yaran da iyaye sun fuskanci tarin matsaloli ne sakamakon raguwar tallafin da ake samu daga ƙasashen duniya, inda manyan ƙasashe masu bayar da tallafi da suka hada da Amurka da Birtania da kuma Tarayyar Turai suka rage kudaden da suke bayarwa.
Ana iya tuna cewa a wannan makon nan da muke bankwana da shi ne Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (WFP) ta sanar da dakatar da tallafin abinci na gaggawa ga mutane milyan 1.3 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya daga karshen watan Yuli, sakamakon karancin kudade.
Ƙungiyar ta ce adadin yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki wanda ya fi kamari kuma mai barazana ga rayuwa a Jihar Katsina ya karu da fiye da kashi 200 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Katsina tamowa yunwa
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura
Shugaban Ƙasar Gambiya, Adama Barrow, tare da matarsa Fatoumata Barrow, sun ziyarci Jihar Katsina, inda suka yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin jajanta wa iyalan marigayin game da rashin da suka yi.
Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasarSun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Faskari, ya tarbe su a madadin Gwamna Dikko Umar Radda.
Bayan sojoji sun yi wa Shugaba Barrow faretin ban girma, sun wuce Daura kai-tsaye, inda suka yi wa iyalan marigayin da kuma Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ta’aziyya.
Ga hotunan a ƙasa: