Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku.

Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12.

Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano

Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku:

Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 50 Na uku: ya zane fuskar mutum fuska 20 cikin mintuna 2 da sakan 55

Ba wannan ne karon farko da ya gwada irin wannan ƙoƙari ba.

A shekarar 2024, ya gwada kafa irin wannan tarihi amma bai yi nasara ba, bayan shafe shekara guda ya sake inganta fasaharsa.

“Na koyi darusa daga gwajin farko. Yanzu na fi yin shiri, na mayar da hankali kuma na dage. Tare da taimakon dana samu, na yi imanin za mu iya kafa tarihi,” in ji shi.

A cewarsa, zanen fuska ba kawai nishaɗi ba ne, fasaha ce da ke nuna al’adu da ƙirƙira.

Ya ce burinsa shi ne ya sanya Kano da Najeriya a idon duniya ta hanyar nuna cewa matasan Najeriya na iya kafa babban tarihi.

Kamfanin Indomie da ya ɗauki nauyin gudanar da gwada bajintar ɗalibin, ya bayyana cewa zai ci gaba da tallafa wa matasan Najeriya don cimma burinsu.

Mutane da dama ciki har ɗalibai da masu kallo sun nuna farin cikinsu.

“Ina fatan Collins zai yi nasara domin ya yi abin a zo a gani,” in ji ɗalibi a BUK, Sulaiman Haruna.

Wani da ya halarci taron, Jimoh Momoh, ya ce Collins ya nuna bajinta kuma ya cancanci yin nasara.

Yanzu dai ana jiran mahukuntan Kundin Tarihi na Duniya na ‘Guinness World Records’ su tabbatar da nasarar ɗalibin.

Idan ta tabbata, ɗalibin zai shiga cikin sahun masu riƙe da kambun tarihi na duniya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibi Tarihi zane fuskar mutum

এছাড়াও পড়ুন:

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Da yake bayanin kan hukumar “Ya ce da akwai rashin bayani dangane da ita hukumar NELFUND, wasu dalibai basu san da akwai ta ba. Akwai kuma wani tunanin da mutane suke yi mi zai sa su tafi makaranta akan bashi?

“Mutane da yawa basu son amsar bashin.Don haka idan mutane basu da yawa, wannan ba kuma yana nufin kamar gwamnatin ta gaza bane, lamarin ya kasance ne domin mutane da yawa basu bukatar neman a basu bashin. Yayin da nake wannan maganar, mai kulawa da harkokin dalibai ya ce akwai dalibai fiye da 3,000 da suke amfana daga shi tsarin na bada bashin kudin makaranta kamar dais hi mataimakin Shugaban Jami’ar ya bayyana,” the BC said.

Da yake bayyana Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya dake Akure , FUTA a matsayin wadda tafiya tare da ita ne a duniya dangane da harkar data shafi ilimi, Farfesa.Oladiji ya ce, makarantar tana tafiya tamkar yadda mutane suke tunanin ko kallonta a matsayin wani wuri ne da ake samun ilimin Boko mai nagarta kamar yadda ya dace,bugu da kari kuma wani wuri ne inda mutum yake daukar mataki na irin yadda yake bukatar cikin ikon Allah ya kasance na dukkan wasu lamurran da suke da alaka da abubuwan da suka shafi karatu gaba daya.

‘’Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya Akure babbar makaranta ce da ta yi suna musamman ma ta bangaren bincike kan lamurran da suka shafi bangaren ilimin fasaha,saboda a samu damar cimmar irin matsalolin da al’umma da duniya suke fuskanta.Hakan abin yake idan aka, tuna da lamarin daya shafi sauyin yanayi da kuma ilimin kimiyyar samaniya,aikin gona, Injiniya, Komfuta da kuma kwarewar lamarrran kafafen sadarwa na zamani.

“A Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya Akure FUTA, mambobi na sassan ita Jami’ar da daibai suna kara kasancewa masu daraja ne da amfani kan lamurran daban- daban a kan lamarin daya shafi karatu ko bada/ koyar da ilimi a duniya, inda suke kasancewa sai an yi tafiya tare da su musamman ma, ta bangaren yin bincike da sanin yadda za a bunkasa abinda aka gano hanyar da za ayi shi. Hakanan ma FUTA bata tsaya ta yi kasa a gwiwa ba domin kuwa tana bada gudunmawa wajen karin haske kan hanyoyin da za abi wajen samar da isasshen abinci a Nijeriya kamar dai yadda Oladiji ya yi nashi karin hasken,”.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ilimi NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu November 8, 2025 Ilimi Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu October 18, 2025 Ilimi Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma October 18, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA
  • Yadda Za Ku Gyara Kanku
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94
  • HOTUNA: Yadda Babban Taronjam’iyyar PDP ke gudana
  • Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja