2025-11-22@22:55:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2773
«Makarantun kwana»:
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar. Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar. Aminiya ta rawaito...
Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci...
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo....
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a...
Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma...
Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta...
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama,...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna...
Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da...
An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku...
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali. Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara. An...
Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala. Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana...
Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985. A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo...
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock...
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock...
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock...
Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda zai iya barin Bayern Munich a bazara mai zuwa.(Star), external Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce Kane, wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din, ‘za su karbe shi da hannu biyu” idan ya dawo , amma ba ya tsammanin dan wasan zai bar kungiyarsa...
Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027. Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da suka ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace...
Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar. Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren ’yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati...
Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula.
Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula. Rundunar Sojoji da ma’aikatan kwalejin su ta Jaji, ta kammala wani shiri na musamman wanda ke nuna wa ‘yan jarida da sauran masu halartar atisaye, sani da gogewar al’amuran yau da kullum...
Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ya gana da tsohon shugaban riƙo na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya). Ya fadar ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya gana da...
Bako wacce ta bayyana hakan bayan ta duba ɗaya daga cikin cibiyoyin CBT, ta ce, ana gudanar da jarrabawar a cibiyoyi uku da aka keɓe, da suka haɗa da Jami’ar Jihar Kaduna a shiyya ta 2), Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya (Shiyya ta 1) da Jami’ar Jihar Kaduna ta Kafanchan (shiyya ta 3). ...
“Bayan tattaunawa mai yawa, aka samu damar tara ₦100,000, wanda ya biya a cikin asusun da masu garkuwa da mutanen suka bayar, bayan wata ɗaya, sai aka bukaci ya biya wani Abdulmajid Dan-Azumi karin ₦10,000, ba tare da sun saki yaron ba,” Abiodun ya bayyana. Waliyyin da ya fahimci lamarin ba mai ƙarewa ba...
Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama. Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025) Shaidu sun...
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan. Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya. UNGA: Yau Shettima zai gabatar da...
Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha...
Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar. ...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan...
Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne...
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyyar Kanada, ƙarfafan tattalin arziƙi, hakar ma’adinai ta hanyar da ta dace, da kuma harkokin kasuwanci masu zaman kansu masu kirkire-kirkire sun sanya ta zama abokiyar haɗin guiwar da ta ta dace ga Afrika. Ya ce, “Idan Afrika za ta cika burinta gaba...
Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai. Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu...
A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan...
Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya. Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya...
Mataimakin shugaban jami’ar ya ja hankalin gwamnati da cewa, yawan al’ummar Nijeriya kusan miliyan 230, kusan kashi 30 cikin 100 na matasa ne a halin yanzu ke makaranta ko kuma suke koyon sana’o’i. Don haka, ya yi gargadin cewa, hakan ya bar wani kaso mai tsoka na matasa da ba su zuwa makaranta ko...
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya...
Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar. Da yake...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa...
“A wani ɓangare na wannan dubarar, jam’iyyar a ƙarƙashin kulawar ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati, ta yi ƙoƙarin shirya zaɓen jagoranci ƙungiyar Musulmai ƴ an asalin Jihar Filato a cibiyar Azi Nyako da ke Dadin-Kowa a garin Jos, wanda daga bayanan da aka samu lamarin ya kasa samun nasara. “PDP na ganin cewa da...
A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65. A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024. Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan,...
’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum. Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja. Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu...
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF. A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar. Ya ce: “Tun...
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar...
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno. Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe. Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu...
Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar...
A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu...