Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi
Published: 21st, November 2025 GMT
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25.
Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare.
“An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris.
Ya ce bayan barin makarantar da sojoji suka yi ƙasa da awa guda ’yan bindiga suka kai hari.
Ya ce barin makarantar da sojojin suka yi, ya saɓa wa alƙawuran da aka yi na ƙarfafa tsaro a makarantu da ke kan iyakar jihar.
Idris, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya da ta jihar na aiki tuƙuru don ceto ɗaliban da aka sace.
Gwamnan, ya bayyana cewa an umarci malaman addini da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da kuɓutar da waɗanda aka sace.
Idris, ya ce abin da ya faru na nuna cewa akwai maƙiya da ke ƙoƙarin kawo cikas ga ci gaban jihar.
A yayin ziyarar nuna goyon baya, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce abin da ya faru abin damuwa ne, musamman ma a lokacin da Kebbi ke samun ci gaba mai kyau.
Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba, kuma ya shawarci gwamnan da ya dage.
Ajaero ya ce, “Wannan kawo cikas ne, amma duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba. Muna tare da ku.”
A halin yanzu, rundunar sojin ƙasa ta fara bincike kan dalilin da ya sa sojojin da aka tura makarantar suka bar wajen aiki kafin aukuwar harin.
Majiyoyin tsaro sun ce a yanzu haka an fara binciken wasu manyan jami’ai kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Gwamna Idiris hari bar makarantar makarantar da
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.
Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba.
NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’ummaWannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan