Gwamnatin Katsina Ta Umurci a Gaggauta Rufe Dukkan Makarantun Jihar
Published: 22nd, November 2025 GMT
Daga Isma’il Adamu
Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati, da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Sani Danjuma, ya sanyawa hannu, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin nuna jajircewar gwamnati wajen kare ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu.
Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantun na iya kawo cikas ga iyaye da ɗalibai, tsaro ya fi komai muhimmanci yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a makarantu.
Ta kuma bukaci hukumomin makarantu da su tabbatar da bin umarnin, tare da kiran iyaye da su ba da haɗin kai, a yayin da gwamnati tare da hukumomin tsaro ke ci gaba da sa ido kan al’amuran domin yiwuwar sake duba wannan mataki.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Rufe Makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja.
Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya.
DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna KebbiShugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba.
Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba.
Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce: “Arewa na fama da ƙalubalen ilimi kuma ba za mu bari miyagu su lalata ci gaban da ake samu ba.”
Ya bayyana damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a makarantu yayin da gwamnatocin Arewa ke ƙoƙarin samar da ingantattun tsare-tsaren tsaro ga ɗalibai.
Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da al’umma don ƙarfafa tsaro a unguwanni da makarantu, da kuma tattara bayanai masu muhimmanci.
A madadin gwamnonin, Gwamna Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka sace da Gwamnatin Jihar Neja.
Ƙungiyar ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa don ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da kuma hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Haka kuma, ta yaba wa jami’an tsaro da ke aikin ceto ɗaliban da malamai, inda ya roƙe su da su ƙara himma, tare da roƙon jama’a su ba da haɗin kai don samun nasarar ceto waɗanda lamarin ya shafa.