’Yan Sanda a Zamfara Sun Ceto Mutane 25 Bayan Dakile Harin ’Yan Bindiga a Damba
Published: 22nd, November 2025 GMT
Daga Aminu Dalhatu
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau.
Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar mata 10 da yara 15 domin tafiyada su.
Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka na Gusau tare da hadin guiwar jami’an tsaro na sa kai wato Community Protection Guards (CPG) sun hanzarta isa yankin.
Jami’an sun bi diddigin ’yan bindigar da suka tsere sannan suka shiga wani salon aiki na dabaru wanda ya kai ga kubutar da dukkan mutanen da aka sace.
DSP Abubakar ya ce an garzaya da wadanda aka ceto zuwa Sabongari Damba domin tabbatar da tsaronsu, duba lafiyar su da tantance su kafin a mika su ga iyalansu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jinjinawa jarumta da kwarewar jami’an da suka gudanar da aikin.
Ya kuma tabbatar da kudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Yan bindiga Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar: Dubban Mutane Sun Tarbi Janar Thiani Bayan Komarwa Birnin Yamai
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin.
Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.”
A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido.
Ana daukar wannan ziyarar ta shugaban kasar a fadin kasar a matsayin kokarin sake tabbatar da hadin kai a tsakanin al’ummar kasar.
Fiye da shekaru 10 kenan Jamhuriyar Nijar take fuskantar matsalolin ta’addanci.
Wani mai fafutukar, Dr.Iro Tanimou ya fada wa manema labaru cewa, ziyarar da shugaban kasar ya kai a fadin kasar, yana nuni ne da sadaukar da kansa,kuma abin alfahari ne yadda ya ziyarci wurare da suke akan iyakokin Burkina Faso da Aljeriya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka Taron G-20 Ba Zai Yi Wani Tasiri Ba November 22, 2025 Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana November 22, 2025 Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci