An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
Published: 7th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno.
Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici.
Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi IIKakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.
Ya ce an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke hada-hadar kayan gwangwan da ke rukunin masana’antu na Kudandan da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.
“Wasu kwararrun jami’anmu daga sashen da ke kula da abubuwa masu fashewa ne ya je wajen bayan bayanan. Bayan cikakken bincike, an tabbatar da cewa kayan bama-bamai ne da ba su kai ga fashewa ba,” in ji Mansir.
Kakakin ya ce nan take jami’an nasu suka kwashe bama-baman zuwa wajen da ya dace sannan suka lalata su ba tare da sun fashe ba.
Ya kuma ce yayin aikin, dakarun sun gano makamai, cikin har da wata karamar bindiga kirar gida wacce ke makare da albarusai, da ma wasu tarin makaman.
Kakakin ya ce nan take Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabiu Muhammad ya bayar da umarnin rufe kamfanin da aka sami kayan domin a samu damar fitar da dukkan makaman ba tare da an bar ragowa ba.
Kwamishinan ya kuma gargadi masu sana’ar ta gwangwan da su daina kawo irin kayayyakin daga yankunan da suke fama da rikici zuwa jihar ta Kaduna.
Ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike domin gano tushen makaman da kuma dalilin shigo da su cikin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.
Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.
An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AINBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024.
Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da man fetur da kuma fannin ma’adinai.
NBS ta ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna ƙarin kashi 19.23 cikin 100.
A watan jiya na Agusta ne Majalisar Ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya, ta sanar da amincewa da sabon tsarin ci gaban tattalin arziki zango na biyu na tsawon shekaru 5 wato 2026-2030, bayan ƙarewar zangon farko wato daga 2021 zuwa 2025.
Sabon tsarin da majalisar ta ƙaddamar wadda ke ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shetima ci gaban tattalin arziki zai yi la’akari da sauye-sauyen da aka samu kamar cire tallafin man fetur, sabbin dokokin haraji da makamatansu.
Ƙarƙashin sabon tsari ne kuma gwamnatin ke son cimma ƙarfin tattalin arziƙi na Dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030, abinda ya dace da manufofin ƙasar har zuwa shekarar 2050.