Yau Juma’a ake bikin nada sabon Olubadan na Ibadan
Published: 26th, September 2025 GMT
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja.
Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Dattawa ’Yan asalin Ibadan (CCII), Cif Ajeniyi Ajewole ya ce, dukkan attajirai ’yan asalin Ibadan an dora masu haraji daga Naira miliyan 10 zuwa sama a matsayin gudunmawarsu ga wannan biki da aka fara da addu’ar rokon Allah a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce, “mun kammala shirin yin bukukuwan nada sabon Olubadan da ba a taba yin irin sa a baya ba, inda za mu shafe mako daya cif ana yi a wurare da lokuta daban-daban a Ibadan.
Haka kuma a matsayinsa na Attajirin mai kudi dan kasuwa da ya taba zama Sanata kuma tsohon Gwamnan Jihar Oyo ya cancanci samun wannan girmamawa a yanzu da ya zama sabon Sarki a Masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 a wannan Jiha ta Oyo”, inji shi.
Kwamitoci biyu da Kungiyar CCII ta kafa, domin tsara bikin na yau Juma’a a karkashin jagorancin Injiniya Dotun Sanusi da Cif Adegboye Adegoke sun yi bayanin cewa, an tanadi jami’an tsaro dubu 2 da aka girke a sassa daban-daban, musamman harabar babban zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin, inda ake yin bikin domin tabbatar da tsaron lafiyar mahalarta da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin isowa da ranar bikin da bayan kammalawa.
Aminiya ta rawaito cewa, kabilun Yarbawa, musamman ’yan asalin Ibadan daga Jihohi 19 na Arewacin kasa a karkashin jagorancin Sarkin Yarbawan Jihar Kano, Ambasada Murtala Alimi Otisese tun cikin makon jiya suka fara isowa gidajensu a sassa daban-daban na Masarautar Ibadan, domin halartar wannan gagarumin biki.
Da yake yi wa Aminiya karin haske, Ambasada Murtala Alimi Otisese a matsayinsa na mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Yarbawan Jihohin Arewa ya ce, “duka Sarakunan Yarbawan Arewa tare da iyalinsu da ‘yan uwa da abokan arziki da muke zaune a ciki da wajen Nijeriya, mun iso nan birnin Ibadan tun kafin isowar wannan rana, domin halartar wannan gagarumin bikin mika wa ubanmu, Oba Rashid Adewolu Ladoja sandan sarauta a matsayin Olubadan na 44 a Masarautar Ibadan.
Wallahi mun yi matukar farin ciki da irin bayanan da Oba Rashid Ladoja ya rika yi tun kafin isowar wannan rana, inda yake cewa, a zamanin mulkinsa za a samu ci gaba a Masarautar Ibadan da Jihar Oyo da kasa baki daya, musamman wajen lalubo hanyar kyautata tsaro a wannan sashe’’.
Ya ce, zai gayyaci bakin ’yan kasuwa na ciki da da wajen Nijeriya, domin zuba jarin kasuwanci da zai bunkasa tattalin arzikin Jihar Oyo da kasa baki daya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: a Masarautar Ibadan
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
A yau Jumma’a 10 ga watan Oktoba, an kaddamar da wani shiri na aikin hadin gwiwa mai lakabin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) na shekarar 2026 a birnin Beijing.
Shen Haixiong, babban darektan CMG, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, CMG ya samu damar zamowa kan gaba a fagen yada labarai na kasa da kasa bisa kayayyakin aiki da ma’aikata, kuma shi ne muhimmin dandali na tallata kayayyakin kasar Sin. Kamfanin a shirye yake ya dauki shirin a matsayin wata damar yin aiki kafada da kafada da abokan kawance daga kowane bangare na rayuwa, tare da rubuta sabon babi a fagen gina kasa mai kunshe da kayayyakin kamfanonin da suka kasance a kan gaba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA