2025-11-20@14:58:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9163

«Gwamnati Kaduna»:

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas...
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza....
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya  domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen...
    Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda...
    Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman ma game da rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Addis...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.  
    Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao. Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu...
    Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba. Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba. Osimhen ba zai halarci...
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu...
    Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400 Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan...
    An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar...
    An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20...
    Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano,...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe...
    pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman...
    Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya.  Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar...
    Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai. Harin an kai shi ne kan sansanin yan...
    Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    A wani lokaci yau Laraba ne aka shirya shugaban majalisar dokokin Togo zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow. Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu, wadanda suka dade suna da kyakkyawar dangantaka, za ta mayar da hankali kan zaman lafiya da tsaron yankin, da kuma batutuwa daban-daban, tun daga da makamashi zuwa ciniki da noma....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.   Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin...
    A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin...
    Dan wasan gaban Manchester United, Benjamin Sesko zai yi jinyar makonni huɗu, lamarin da zai hana shi buga wa ƙungiyar wasanni shida a jere. Šeško mai shekaru 22, ba zai samu damar taka leda ba a wasan da United za ta karɓi baƙuncin Everton a Old Trafford mako mai zuwa. Gwamnan Taraba ya dakatar da...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane...
    Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse. Anthony Joshua zai yi...
    Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na...
    A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata. Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar. Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici...
    Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa. Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya...
    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa...
    Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza. An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na...
    Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai da kuri’ar amincewa da kudurin Amurka da aka yi a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na aikewa da dakarun kasashen waje zuwa yankin Gaza yace wannan baban abin kunya...
    An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban...
    “Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari...
    Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza. Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar. Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje...
    Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen...