Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar
Published: 20th, November 2025 GMT
Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta.
An fitar da wannan sanarwa ce a shafin x na micheal achimugu daraktan kula da hulda da jama’a da kula da fasinjoji, ya kara da cewa wannan hukumci ya sanya adadin kamfanonin jiragen sama da aka ci tara sun kai guda 7 a wannan shekarar ta 2025
Hukumar NCAA ta zargi kamfanin jiragen sama na Qatar airways a watan satumban shekarar da muke ciki da take dokokin kula da hakokin fasinjoji da kuma yin mummunar muamala da fasinjonin ta yan najeriya
Haka zalika hukumar ta yi Gargadin kakabawa kafanin jirgin saman takunkumi idan ya ci gaba da keta dokokin hukumar jiragen sama ta kasar. Hukumar ta ta bayyana cewa a 28 ga watan decembar shekara ta 2024 ta sanya takunkumi kan kamfanin jiragen sama na air peace, Ethiopian airline, Arik Air, Aero contractos da kuma royala air maroc saboda taka dokokin hukumar da ta gindaya a bangare na 19.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza November 20, 2025 Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa November 20, 2025 Achraf Hakimi Ya Zama Gwarzon Wasan Kwallon Kafar Afirka Na Shekara Ta 2025 November 20, 2025 Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini November 20, 2025 Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam November 20, 2025 Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu November 20, 2025 AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Amurka ta Shawarci Ukraine ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye mata November 20, 2025 Sudan ta yaba da kokarin Amurka da Saudiyya na kawo karshen rikicin kasar November 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kamfanin jiragen sama na jiragen sama ta
এছাড়াও পড়ুন:
An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa.
Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a NajeriyaDSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012.
Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan sanda na Unguwa Uku, da wasu wurare.
Mutane da dama sun jikkata a yayin kai waɗannan hare-hare.
An kama Ismaila ne a ranar 31 ga watan Agustan 2017, a ƙauyen Tsamiyya Babba da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, a Jihar Kano.
Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokar hana aikata ta’addanci ta 2013.
Shari’ar ta ɗauki lokaci saboda ɗaukaka ƙara da kuma tabbatar da bayanan da ya bayar da farko ba tursasa shi aka yi ba.
A ƙarshe, lauyoyin gwamnati sun kira shaidu biyar, ciki har da jami’an DSS da mutanen da harin ya shafa.
Da farko Ismaila, ya ƙi amincewa da laifin da ake tuhumarsa amma bayan gabatar da shaida na biyar, ya sauya maganarsa ya amsa laifin.
Lauyansa daga Hukumar LAC, P. B. Onijah, ya roƙi kotu ta yi masa sassauci, inda bayyana cewa Ismaila ya nuna nadama kuma bai son ɓata wa kotu lokaci.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya yanke masa shekar 15 kan tuhumar farko da kuma shekaru 20 kan sauran kowace tuhuma uku.
Dukkanin hukuncin za su tafi a lokaci guda, kuma za su fara aiki tun daga ranar da aka kama shi a shekarar 2017.
Alƙalin ya umarci Hukumar Gyaran Hali ta tsare shi a gidan yari da Babban Kwamandan Hukumar ya zaɓa.
Bayan ya kammala zaman gidan yari, dole a yi masa horon gyaran hali da kawar da ra’ayin ƙiyayya kafin a sake mayar da shi cikin al’umma.