Aminiya:
2025-10-13@17:53:37 GMT

Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano

Published: 25th, September 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni a 2027 — Atiku

Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa, wanda ake zargin ya yi zazzafar taƙaddama da kakansa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75 da kuma kakarsa, Hadiza Tasidi mai shekara 65, inda ake zargin ya kai musu farmaki da wuƙa, tare da jikkata su da dama.

An garzaya da dukkan waɗanda suka rasu zuwa asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu. Daga baya aka miƙa gawarsu ga ’yan uwa domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

SP Kiyawa ya bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mai yiwuwa wanda ake zargin ya sha kayan maye a lokacin da lamarin ya faru.

Ya kuma bayyana cewa, Kwamishinan ’yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin miƙa ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), domin gudanar da bincike mai zurfi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda ya kashe kakanninsa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari

Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano
  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
  • Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari
  • Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano